Kungiyar Gwamnoni Ta Zabi Gwamna 1 da Ya Fi Kowa Kokari a 2025
- Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ba Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom lambar yabo ta gwamna mafi kokari a shekara ta 2025
- An bayyana cewa jihar Akwa Ibom ta fi kowace jiha a Najeriya a fannin kyakkyawan mulki, tsare-tattalin arziki da samar da ci gaba
- Gwamna Eno ya sadaukar da kyautar ga al’ummar jiharsa tare da alkawarin ci gaba da gudanar da mulki mai maida hankali kan jama’a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta karrama gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom a matsayin gwamnan shekarar 2025.
Wannan karramawa ta zo ne sakamakon jagoranci na gaskiya, tsare-tsaren ingantaccen mulki da kuma nasarorin da ya cimma ta hanyar shirin Arise Agenda.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa an gabatar da lambar yabon ne a dakin taro na fadar gwamnati ta Uyo, ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
Sabon shugaban APC da gwamnoni sun gana da Sheikh Jingir, malaman Izala da Darika
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Abba Gambo da ya wakilci Darakta Janar na NGF, Abdullateef Shittu, ya bayyana cewa jihar Akwa Ibom ta samu matsayi na farko a jerin gwamnatoci masu nagarta da tsara tattali.
Umo Eno ya zama gwamna na 1 a 2025
A cewar NGF, nazarin gwamnatoci jiha-zuwa-jiha ya nuna cewa Akwa Ibom ta yi fice a fannin mulki, amfani da kudi da kuma yin da manyan ayyuka ga al’umma.
Abin lura shi ne, duk wadannan nasarori an cimma su ne ba tare da karbar bashi daga bankuna ko wata hanyar aro daga waje ba.
This Day ta wallafa cewa Farfesa Gambo ya ce:
“Abin farin ciki ne a gare mu a NGF mu bai wa Mai Girma, Fasto Umo Eno, wannan lambar yabo ta gwamnan shekarar 2025.”
Ya kara da cewa irin wannan nasara ba kasafai ake samunta a wannan yanayi na tattalin arzikin kasar ba.

Kara karanta wannan
Gwamna ya amince a kashe N1bn a fannoni 3, za a sayo littattafan N588m a jihar Katsina
Gwamna Eno ya sadaukar da lambar yabon
A jawabinsa, gwamna Umo Eno ya sadaukar da lambar yabon ga al’ummar Akwa Ibom, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bin tsari mai gaskiya da maida hankali kan bukatun jama’a.
“Wannan karramawa ta kara mana kwarin gwiwa. Za mu ci gaba da amfani da dukiyar jihar Akwa Ibom wajen gina abubuwan more rayuwa, karfafa al’umma da gina makoma mai kyau,”
- In ji shi
Ya bayyana cewa nasarorin da aka samu na da nasaba da tsare-tsaren amfani da kudi yadda ya kamata, sauye-sauyen cibiyoyi da kuma bin tsari mai inganci.

Source: Facebook
Yadda aka karrama Gwamna Eno
Taron karramawar ya kunshi tattaunawa kan manufofi, nazarin kwararru da gabatar da rahotanni kan ci gaban da jihar ta samu a cikin shekara biyu.
Cikin wadanda suka halarci taron akwai jami’an gwamnatin tarayya, ministoci, kwararrun masana tattalin arziki, kungiyoyin raya kasa, kungiyoyin farar hula da ‘yan jarida.
An kama boka a jihar Akwa Ibom

Kara karanta wannan
APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi nasarar kama wani boka a jihar Akwa Ibom.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin bokan da aka kama da sayar da maganin bindiga wa 'yan fashi da makami.
Kakakin 'yan sandan jihar ta bayyana cewa sun samu bindiga kirar gida a wajen shi, lamarin da ke nuna yana da alaka da 'yan ta'adda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng