Najeriya Ta Sake Nunawa Trump Jan Wuya kan Karbar 'Yan Ciranin Amurka

Najeriya Ta Sake Nunawa Trump Jan Wuya kan Karbar 'Yan Ciranin Amurka

  • Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta karɓi mutanen da aka kora daga Amurka ba, sabanin kasashen Rwanda, Eswatini da Kudancin Sudan
  • Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya ce matsayar kasar ta ta’allaka ne kan batun tsaro da tattalin arziki
  • Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya ce shirin karɓar fursunonin ƙasashen waje daga Amurka ba zai yiwu a Najeriya ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da matsayarta na ƙin amincewa da shirin karɓar bakin da aka kora daga Amurka.

Najeriya ta fadi haka ne tana nisantar kanta daga matakin da wasu ƙasashen Afirka suka ɗauka, ciki har da Rwanda, Eswatini da Kudancin Sudan.

Najeriya ta jaddada kin karbar 'yan ciranin Amurka
Najeriya ta jaddada kin karbar 'yan ciranin Amurka. Hoto: Donald Trump|Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Punch ta wallafa cewa kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya ce kasar ba za ta lamunci shirin ba saboda matsalolin tsaro da tattali da take fuskanta a halin yanzu.

Kara karanta wannan

'Najeriya ka iya wargajewa kafin zaɓen 2027': Tsohon minista ya yi hasashe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a baya, ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa gwamnatin Donald Trump tana matsa wa ƙasashen Afirka lamba su karɓi bakin da aka kora daga Amurka.

Najeriya ta ki karbar 'yan ciranin Amurka

A watan Yuli Tuggar ya bayyana cewa Amurka na ƙoƙarin tilasta wasu ƙasashen Afirka su karɓi 'yan cirani, musamman fursunonin Venezuela, da za a kora daga Amurka kai tsaye daga kurkuku.

Ministan ya ce ya ce wannan mataki ba zai yiwu a Najeriya ba, domin kasar na da nata kalubalen da ya ishe ta.

Rahotanni sun nuna cewa shirin ya samu nasara ne bayan kotun kolin Amurka ta amince da shi a ranar 23 ga Yuni, 2025.

Hakan ne kuma ya bai wa gwamnati damar tura bakin da aka kora zuwa wata ƙasa dabam in har ƙasarsu ta ki karɓar su.

Kasashen da suka yarda da bukatar Trump

Kudancin Sudan ce ta farko a Afirka da ta amince da shirin, inda aka tura mata mutane takwas da aka yankewa hukunci kan laifuffuka masu tsanani.

Kara karanta wannan

Jiragen yaki sun kona 'yan bindiga kurmus suna bikin aure a dajin Zamfara

Rahoton CCN ya nuna cewa daga bisani Eswatini ta karɓi wasu daga Vietnam, Jamaica, Cuba, Yemen da Laos.

Rwanda ta rattaba hannu kan yarjejeniya da ta ba ta damar karɓar bakin da aka kora har 250 daga Amurka, amma tana da ikon tantance waɗanda za ta karɓa.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Dalilin Najeriya na ƙin amincewa da tsarin

Ebienfa ya ce duk da cewa wasu ƙasashen Afirka sun amince da wannan shiri, Najeriya za ta ci gaba da tsayawa kan matsayarta.

Ya bayyana cewa:

“Ko da sauran ƙasashen Afirka sun amince da shirin, Najeriya ba za ta amince ba. Muna da ikon yanke matsaya bisa abin da zai amfanar da tsaronmu da tattalin arzikimmu.”

Donald Trump ya laftawa Najeriya haraji

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya kakaba wa kasashe haraji bayan wa'adin da ya bayar ya cika.

A watannin baya shugaba Trump ya kawo sabuwar dokar haraji, amma ya dakatar da it zuwa watan Agustan 2025.

A farkon Agusta ne shugaban ya laftawa Najeriya haraji da kashi 15, tare da daukar irin matakin kan wasu kasashe dabam.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng