Babu Boye Boye, An Ji Halin da Tsohon Shugaban APC, Ganduje ke ciki a Landan
- Tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya tafi Landan ne domin ya samu hutu bayan kammala aikin da aka ɗora masa
- Malam Muhammed Garba, tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Kano ne ya bayyana hakan kusan watanni biyu bayan Ganduje ya yi murabus
- Ya ce Ganduje ya tafi Landan ne domin wasu abubuwa na ƙashin kansa wanda aka tsara tun kafin ya ajiye shugabancin APC mai mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Tun bayan murabus dinsa daga kujerar shugaban APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya shirya ya bar Najeriya zuwa birnin Landan na ƙasar Ingila.
Wannan ya sa aka fara yaɗa jita-jitar cewa Ganduje ya tafi jinya ne a asibiti saboda ya ambaci rashin lafiya a matsayin dalilinsa na yin murabus.

Kara karanta wannan
Rigima ta ɓarke tsakanin Shugaba Tinubu da Ganduje ana shirin 2027? An samu bayani

Source: Facebook
Tsohon kwamishinan yaɗa labarai a Kano, Muhammed Garba ya tabbatar wa Daily Trust cewa Ganduje ya ajiye shugabancin APC ne saboda kula da lafiyarsa amma abin bai yi tsanani ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin Abdullahi Ganduje na tafiya Landan
Muhammed Garba, wanda Ganduje ya naɗa a matsayin shugaban ma'aikatansa a lokacin da yake jagorantar APC, ya ce tsohon gwamnan ya tafi Landan ne don ya samu hutu.
Ya ce bayan kammala ayyukan da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ɗora masa, Abdullahi Ganduje ya ga ya dace ya je duba lafiya kuma ya huta a birnin Landan.
"Ganduje ya bar Najeriya zuwa Ingila kwana biyar bayan murabus dinsa daga matsayin shugaban jam’iyyar APC, kuma idan ka tuna, ɗaya daga cikin dalilan da ya bayar shi ne batun lafiyarsa.
"Sai dai ba wata matsala mai tsanani ba ce; yana bukatar ya huta bayan irin hidima da aiki tuƙuru da ya yi wajen nasarar jam’iyya da ci gaban ƙasa," in ji shi.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II ya yi maganar halin da ake ciki, ya ɗauko tarihin sama da shekaru 10
Me ya hana Ganduje zuwa tarbar Tinubu?
Hadimin tsohon gwamnan ya kare maigidansa kan rashin ganinsa a wurin tarbar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Kano.
Ya tabbatar da cewa Ganduje ba ya Najeriya a lokacin amma ya yi ƙoƙarin dawowa duk da hakan ya ci tura.
"Yana birnin Landan lokacin da Dantata ya rasu, don haka ba ya gida ballantana ya samu damar zuwa tarbar Shugaban Ƙasa lokacin da ya kawo ziyarar ta’aziyya.
"Haka kuma, lokacin da mutane suka fara surutu, na fito na bayyana abin da ya sa ba a ga Ganduje ba"
"Waus na yaɗa cewa yana kwance yana jinya, ko an hana shi zuwa kusa da shugaban ƙasa, duk ba haka ba ne, Ganduje ya tafi Landan ne domin wani lamari na ƙashin kansa, wanda aka tsara tun kafin lokacin.
- Muhammed Garba.

Source: Twitter
Rigima ta shiga tsakanin Ganduje da Tinubu?
A wani labarin, kun ji cewa hadimin tsohon shugaban APC ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa Dr. Abdullahi Ganduje da Shugaba Tinubu sun ɓata.
Tun lokacin da Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC, aka fara yaɗa jita-jitar cewa alaƙarsa da Shugaba Tinubu ta yi tsami
Sai dai Muhammed Garba ya ce mutane na da ƴancin faɗar duk abin da suke so, amma babu wani saɓani da ya shiga tsakanin Ganduje da Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
