Ana Murnar Za a Samu Sauƙi, Matatar Ɗangote Ta Canza Farashin Fetur a Najeriya
- Yayin da ake murnar za a sanu sauƙi bayan kamfanin NNPCL ya rage farashin man fetur, matatar Ɗangote ta ƙara N30 kan kowace lita ga ƴan kasuwa
- An ruwaito cewa matatar Ɗangote da ke jihar Legas ta ƙara farashin litar fetur daga N820 zuwa N850 a rumbunan ajiya da take sayarwa ƴan kasuwa
- Shugaban ƙungiyar dillalan man fetur (IPMAN) na ƙasa, Abubakar Garima ya tabbatar da wannan ƙari a yau Juma'a, 8 ga watan Agusta, 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Matatar hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Dangote ta ƙara farashin da take sayar wa ƴan kasuwa man fetur a Najeriya.
Matatar Ɗangote ta ƙara farashin kowace lita zuwa N850 a rumbunan ajiyarta, wurin da take sayarwa dillalan fetur da ke kasuwancinsa a faɗin ƙasar nan.

Source: Getty Images
Jaridar The Cable ta tattaro cewa wannan sabon farashi ya nuna ƙarin N30 daga tsohon farashin kowace lita N820.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matatar Ɗangote ta kara farashin fetur
Ƙarin farashin fetur a rumbunan ajiya na nufin ‘yan Najeriya da kamfanoni za su biya ƙarin kuɗi don samun wannan kayayyaki a gidajen mai ko hannun ƴan kasuwa.
A ranar Laraba, rahotanni sun nuna cewa wasu abokan hulɗar matatar Dangote sun ƙara farashin kowace lita ɗaya a gidan mai zuwa N915 a jihar Lagos.
Shugaban ƙungiyar dillalan fetur ta Najeriya (IPMAN), Abubakar Garima, ya tabbatar da ƙarin da matatar Ɗangote ta yiwa ƴan kasuwa yau Juma'a.
“Sabon farashin da ake sayar mana da man fetur a matatar shi ne N850 a kowace lita," in ji shi.
Ɗangote ya dawo da kasuwanci da abokan hulɗa
Abubakar Garima ya kuma bayyana cewa matatar ta fara sayar da fetur ga abokan hulɗarta bayan hutun mako guda, rahoton Guardian.

Kara karanta wannan
YouthCred: Gwamnatin Tinubu ta kawo shirin da kowane matashi zai iya samun N200,000
A ranar 18 ga Yuli, matatar Ɗangote ta sanar da dakatar da tsarin rangwamen farashi ga abokan hulɗar ta na musamman.
A cewar matatar, an ɗauki wannan mataki ne saboda koke-koken da aka samu cewa wasu abokan hulɗar suna sayar da haƙƙin karɓar kaya ga wasu ƴan kasuwa.

Source: Getty Images
A makon da ya gabata, matatar ta umarci ‘yan kasuwa da su dakatar da duk wani biyan kuɗi domin ɗaukar man fetur daga rumbunan ajiyarta.
Wannan ƙari da aka samu a matatar Dangote ya zo ne kwanaki kaɗan bayan kamfanin mai na Najeriya (NNPCL) ya rage farashin litar fetur zuwa N875 a Legas, da N900 a Abuja.
Wani dan bunburutu, Sabitu Dogo ya bayyana cewa galibi idan aka yi ragin farashin fetur ba ya zuwa wurin talakawa amma idan kari ne nan take ake yi.
Da yake tattaunawa da wakilin Legit Hausa cewa wannan karin da aka yi ya ba shi mamaki saboda a cewarsa, bai dade ba gidan man NNPL suka yi ragi.
"Shekaran jiya na ji an samu saukin kusan N30 a gidan man NNPC, na yi tsammanin sai dai ya kara sauka ba ya tashi ba, amma matatar Dangote ta rikita lissafin.
"Fetur dai wani abu da zai wahala a daina amfani da shi nan kusa, abu ne ya zama kamar abinci, idan har za a taimaki talaka to ya kamata a sauke farashin fetur," in ji Sabitu.
Kamfanin NNPCL zai sayar da matatar Fatakwal?
Kuna da labarin cewa kamfanin mai na kasa watau NNPCL ya bayyana a hukumance cewa ba zai sayar da matatar fetur mallakin gwamnati da ke Fatakwal a jihar Ribas ba.
Shugaban kamfanin NNPCL, Bashir Ojulari, ne ya bayyana hakan a yayin taron tattaunawa da ma’aikata, ya ce gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da kulawa da matatar.
Jawabin Ojulari ya samu karbuwa daga ɗaruruwan ma’aikatan da suka halarci taron, waɗanda suka nuna farin cikinsu kan wannan mataki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

