Dangote Zai Bude Sabon Kamfanin Siminti, Mutane za Su Samu Aiki a Côte d’Ivoire
- Sabon kamfanin Alhaji Aliko Dangote a Côte d’Ivoire zai rika fitar da tan miliyan uku na siminti a duk shekara
- Za a samar da ayyukan yi kai tsaye ga tsakanin mutum 2,000 zuwa 3,000 a sabon kamfanin da ake kammalawa
- Aliko Dangote ya ce wannan mataki zai taimaka wajen rage shigo da siminti daga waje a yammacin Afirka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kamfanin Dangote wanda shi ne mafi girma a nahiyar Afirka wajen samar da siminti, ya bayyana shirin ƙaddamar da sabon kamfani a ƙasar Côte d’Ivoire,
Rahotanni sun nuna cewa za a samar da kamfanin ne domin cin moriyar cigaban da ake samu a bangaren gine-gine a kasar.

Source: Facebook
Rahoton Bloomberg ya nuna cewa Dangote ya ce sabon kamfanin zai rika fitar da siminti har tan miliyan uku a kowace shekara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga haka, bayanai sun nuna cewa aikin yana dab da kammaluwa tare da shirin fara sarrafa siminti cikin shekarar nan.
Côte d’Ivoire za ta kasance ƙasa ta goma da kamfanin Dangote ke da rassa a cikinta, bayan Najeriya, inda kamfanin ke da asali.
Menene ya ja hankali Dangote a Côte d’Ivoire?
Wani bincike ya nuna cewa kasuwar gine-gine a Côte d’Ivoire za ta ci gaba da habaka da 9.6% duk shekara daga 2025 zuwa 2032.
Ƙasar na zuba jari a manyan ayyukan cigaba kamar makamashi da sufuri, wanda ya sa kamfanin Dangote ya ga ya dace ya zuba jari a bangaren siminti.
A cewar kamfanin, zuba jarin ba masana’antu kawai zai amfana ba, har ma wani mataki ne na ƙarfafa ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.

Source: Getty Images
Dangote zai samar da dubban ayyuka
Tell Magazine ta wallafa cewa kamfanin ya ce sabon katafaren wurin sarrafa simintin zai samar da ayyukan yi kai tsaye ga mutane tsakanin 2,000 zuwa 3,000.
Rahotanni sun nuna cewa hakan zai taimaka wajen fitar da ƙasar daga dogaro da bangare ɗaya na tattalin arziki.
“Wannan matsayi mai muhimmanci da Côte d’Ivoire ke da shi yana cikin burinmu na ganin Afirka ta dogara da kanta wajen samar da siminti,”
- In ji Dangote yayin ƙaddamar da shirin
Ya ce kamfanin na son ganin Afirka ta gina kanta da hannunta, ta hanyar samar da kayayyakin da ke bukata a cikin gida.
Habakar simintin Dangote a Najeriya
Kamfanin simintin Dangote yana samar da isasshen siminti a Najeriya, har ma yana fitar shi zuwa wasu ƙasashen Afirka.
Dangote na shirin gina wani katafaren kamfani a Itori, yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, wanda zai iya fitar da siminti tan miliyan 6 a shekara daga 2027.
Haka zalika, yana shirin tara Dala miliyan 400 a kasuwar kuɗi ta Habasha domin faɗaɗa wani reshe a can.
Kamfanin Dangote zai dauki ma'aikata
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya bude shafin daukar ma'aikata a rukunin kamfanoninsa.
Rahotanni sun bayyana cewa za a dauki ma'aikata ne a fannoni da dama, daga manya zuwa kanana.
An bukaci duk wandanda suka cancanta kuma suke sha'awar aiki da kamfanin da su tura bayanansu a shafin da aka tanada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


