YouthCred: Gwamnatin Tinubu Ta Kawo Shirin da kowane Matashi Zai Iya Samun N200,000

YouthCred: Gwamnatin Tinubu Ta Kawo Shirin da kowane Matashi Zai Iya Samun N200,000

  • Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu Bola Ahmed Tinubu ta kaddamar da shirin ba matasa rance na YouthCred
  • A wannan sabon shiri, duk matashin da ya yi rijista kuma ya cika sharuɗɗan da aka gindaya, zai samu aron kuɗi har N200,000
  • Ministan matasa, Ayodele Olawande ne ya jagoranci kaddamar da shirin, wanda za a fara da matasa ƴan bautar ƙasa watau NYSC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya a ranar Alhamis ta kaddamar da shirin bayar da rance ga matasa mai suna Youth Credit Initiative ƙarƙashin hukumar CREDICORP.

Gwamnatin ta bayyana cewa shirin zai ƙarfafa matasan Najeriya tare da ba su damar da za su farfaɗo da tattalin arzikinsu kuma su dogara da kansu.

Matasan Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin bai wa matasan rance Hoto: @ayowisdom
Source: Twitter

Yadda matasa za su samu rancen N200,000

The Nation ta rahoto cewa a ƙarƙashin wannan shiri, duka matasan da suka cika sharuɗɗan da aka gindaya, za su samu rancen kuɗin mafi yawa N200,000.

Kara karanta wannan

Yadda PDP ke kai kawo wajen lalubo wanda zai gwabza da Tinubu a zaben 2027

Shirin ya tanadi ƙaramin kaso na riba a wurin biyan bashin ƙarƙashin YouthCred wanda CREDICORP ke gudanarwa.

Legit Hausa ta rahoto cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ware wa sabon shirin Naira biliyan 9 a matakin farko.

Haka zalika shirin zai fara da matasa masu yi wa ƙasa hidima watau NYSC a faɗin ƙananan hukumomi 774 da ke Najeriya..

Ministan matasa ya ƙaddamar da shirin

Ministan Harkokin Matasa, Ayodele Olawande, ne ya kaddamar da wannan shiri a ranar Alhamis tare da Darakta Janar na CREDICORP, Injiniya Uzoma Nwagba, a sansanin horar da NYSC da ke Kubwa, Abuja.

A sanarwar da ya wallafa a X, ya ce bayan kaddamar da shirin a hukumance, masu yi wa ƙasa hidima za su iya yin rajista domin samun rancen kudin, sannan daga nan za a horas da su.

Olawande ya kwatanta wannan sabon shirin da irin tagomashin da matasa a ƙasashen da suka ci gaba suke samu da damar da suke da ita na amfani da bashi.

Kara karanta wannan

Kimanin wata 1 da rasuwar Buhari, Adamu Maina ya auna mulkinsa da na Tinubu

Abin da ya sa za fara ba matasa rance

Ya jaddada cewa wannan sabon shiri zai taimaka wajen rage gibin tattalin arziki ga matasan Najeriya.

“A Amurka, saurayi zai iya yin hoto da mota ya yi kama da mai kuɗi, ba saboda yana da miliyoyi ba, sa dai don yana da damar samun rance," in ji shi.
Ministan harkokin matasa, Ayodele Olawande.
Za fara shirin ba matasa rance da ƴan NYSC Hoto: @ayowisdom
Source: Twitter

Olawande ya bayyana cewa abin da yawancin matasan Najeriya ke buƙata ba taimako kai tsaye ba ne, illa dai samun bashi mai tsari da zai taimaka masu a rayuwa.

Ministan ya ci gaba da cewa:

“Wannan ba batun manufofi ba ne, muna magana ne kan ƙarfafa tattalin arziki ta hanyar tsari mai kyau. A karon farko, mun samu shugaban ƙasar da ke sauraron kokenmu, ba mulki kaɗai yake ba, yana jagorantarmu zuwa ci gaba."

Wani matashi, Yahaya Ahmad ya bayyana cewa duk da dai kudin sun yi kadan amma abu ne mai kyau wanda zai taimakawa matasa.

Da yake tattaunawa da wakilin Legit Hausa, matashin ya ce bashin N200,000 ya yi kadan a tsadar rayuwar da ake ciki a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Mene aka yi mana?' Hadimin Ganduje ya ce za su tuhumi Tinubu a Kano

Yahaya ya ce:

"Akwai matasan da suna bukatar jari ko da kuwa ba shi ne, da za su kara a kasuwancinsu, kuma a shirye suke su biya, amma ban da bashi mai ruwa.
"Wannan shiri abu ne mai kyau amma ya yi kadan, muna kira ga gwamnati ta kara tawan kudin kuma ta kawo tsarin rancen da babu kudin ruwa saboda musulmai."

Gwamnatin Tinubu ta buɗe rijistar RHEI

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta fara rajista mataki na biyu na shirin RHEI don rage rashin aikin yi da koyar da matasa sabbin dabaru.

Darakta-Janar na NDE, Silas Agara ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa an buɗe shafin yanae gizo da matasa za su yi rijista daga 28 ga watan Yuli zuwa 11 ga Agusta, 2025.

Ya ƙara da cewa za a fara tantance bayanan waɗanda suka cike daga ranar 12 zuwa 22 ga watan Agusta, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262