Dara Ta Ci Gida: Yadda 'Dan Sanda Ya Tsere da Gudu bayan Kama Kwamishinansu

Dara Ta Ci Gida: Yadda 'Dan Sanda Ya Tsere da Gudu bayan Kama Kwamishinansu

  • Tsohon Sufetan ƴan sanda, MD Abubakar, ya bayyana yadda aka kama shi a Lagos ba tare da an gane shi ba
  • Lamarin ya faru ne a yayin da ya fita duba ayyukan jami'ansa a ofisoshin 'yan sanda a wata ranar Asabar
  • Daga bisani jami’an suka gane cewa wanda suka kama shi ne Kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban su gaba ɗaya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon kwamishinan 'yan sanda na jihar Lagos kuma Sufeto Janar na 'yan sanda a baya, Mohammed Dikko Abubakar, ya bayyana wani abin dariya da ya faru da shi.

A wata tattaunawa da ya yi, MD Abubakar ya bayyana yadda wasu jami'ansa suka kama shi ba tare da sun gane shi ba, bayan da ya saje da mutane domin ya gano halin da suke ciki a bakin aiki.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Bam ya tarwatsa yara 3 suna tsaka da wasa a Borno

Tsohon sufeton 'yan sandan Najeriya, MD Abubakar
Tsohon sufeton 'yan sandan Najeriya, MD Abubakar. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da MD Abubakar ya yi wajen bayar da labarin a sakon da Zagazola Makama ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An taba yawo da wannan labari a shekarun baya. Idan za a tuna, daga baya MD Abubakar sai da ya shugabanci rundunar 'yan sandan Najeriya.

Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani yammaci na ranar Asabar kuma ya nuna irin tsarin jagoranci da kwarewar da ya ke da shi wajen sarrafa lamarin tsaro da mutunta aikin sa.

Yadda aka kama kwamishinan 'yan sanda

A cewar MD Abubakar, zai fita wata ranar Asabar da misalin karfe 10:00 na safe, sai ya yanke shawarar fita da wuri domin ya duba wasu ofisoshin 'yan sanda da ke karkashin kulawarsa.

Ya ce a lokacin yana tuka motarsa ne a kan titin Herbert Macaulay a garin legas, sai ya tsaya a wani shingen bincike da 'yan sanda ke tsare mutane.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun titsiye Sarki a dajin Zamfara, ya amsa tambayoyi masu zafi

Sai wani matashin dan sanda ya dakatar da shi tare da tambayarsa:

“Ina za ka je da motar mahaifinka?”

Daga nan suka bukaci ganin katin shaidar aiki, amma ya ce sai su fara nuna nasu, sai suka yanke shawarar kai shi ofishin ‘yan sanda na Panti a Yaba.

Me ya faru bayan zuwa caji ofis?

A ofishin, sun bukaci ya tsaya a wani wuri amma ba a samu filin ajiye mota ba sai wajen da DPO ke ajiye abin hawa.

Ya bayyana cewa wani dan sanda ya daka masa tsawa yana cewa kada ya ajiye motarsa a wajen DPO.

Daga bisani, wani ASP cikin kayan gida ya ce ya shigo ofishinsa, MD Abubakar ya ki shiga, sai jami'in ya ja shi da karfi.

Wani tsoho da ke wajen ofishin ya shiga ofishin DPO don duba hoton kwamishinan, sai ya tabbatar da cewa shi ne wanda aka kama, nan take ya tsere ta taga.

Yan sandan Najeriya a bakin aiki
Yan sandan Najeriya a bakin aiki. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

MD Abubakar ya bayyana cewa shi ma ASP da ya ke kokarin jan shi din ya tsere ta taga nan take.

Kara karanta wannan

'A murƙushe su kawai': Shehi ya faɗi hukuncin Musulunci kan irinsu Bello Turji

Matakin da kwamishinan 'yan sandan ya dauka

Daga baya sai DPO da ASP da sauran jami’an da lamarin ya shafa sun tsinci kansu a cikin dakin ajiye masu laifi suna jiran hukunci.

Vanguard ta wallafa cewa bayan an kira MD Abubakar domin daukar mataki, ya yanke shawarar yafe musu.

Ya bayyana cewa a ranar Litinin, sama da mutum 100 suka ziyarce shi suna kuka da rokon kada ya kori jami’an 'yan sandan.

DSS sun kama shugaban Mahmuda

A wani rahoton, kun ji cewa an samu rahotanni da suke nuni da cewa an shugaban kungiyar ta'addanci ta Mahmuda.

Kama dan ta'addan ya jawo mutane a jihohi Neja da Kwara sun barke da murna saboda suna fatan za su samu sauki.

Wasu mutane a Neja sun bayyana cewa sun kwana biyu ba su ji duriyar 'yan ta'addan ba, lamarin da ke kara tabbatar da kama shugaban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng