Sarki Sanusi II Ya Yi Maganar Halin da Ake Ciki, Ya Ɗauko Tarihin Sama da Shekaru 10

Sarki Sanusi II Ya Yi Maganar Halin da Ake Ciki, Ya Ɗauko Tarihin Sama da Shekaru 10

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa bai yi mamakin halin da ake ciki ba a Najeriya duk da dai abin damuwa ne matuƙa
  • Ya ce tun farko ya ba da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka don gujewa wannan matsala amma aka ɗauke shi tamkar abokin gaba
  • Mai martaba Sanusi II dai ya sha bai wa gwamnatin tarayya shawarar cire tallafin man fetur tun 2012, amma hakan ba ta yiwuwa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya bayyana rashin jin daɗinsa game da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki.

Sanusi II ya tuna wa ƴan Najeriya maganganun da ya yi kan tattalin arziki a shekarun baya, yana mai cewa bai yi mamakin halin da ake ciki ba a yanzu.

Kara karanta wannan

Ana batun yunwa, gwamnatin Tinubu ta fitar da ton 42,000 na hatsi a raba wa jihohi

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana damuwa kan halin da jama'a ke ciki Hoto: @masarautarkano
Source: Twitter

Basaraken ya faɗi haka ne a shirin Politics Today na tashar Channels tv a ranar Laraba, yayin da yake magana kan rayuwar marigayi Janar Murtala Muhammed.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanusi II ya tuna abin da ya faɗa tun 2012

Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya ce masu ilimin tattalin arzikin ƙasa ba su yi mamakin halin da Najeriya ke ciki ba yau.

Sarkin ya ce:

“Ku duba, na dade ina magana kan tattalin arziki, kuma na yi gargadi sama da shekaru goma da suka gabata cewa nan muka tunkara, ya kamata a ɗauki mataki.
"Ba na zaton wani da ya yi karatun tattalin arziki zai yi mamakin halin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki ba yanzu. Mun shafe shekaru masu yawa muna bin manufofin da za su lalata mana tattalin arziki.

Yadda aka rika watsi da shawarwarin Sanusi II

Sarkin na Kano ya ƙara da cewa a baya duk wani ra'ayi ko shawara da aka kawo, matuƙar ya saɓawa manufofin da aka zo da su, nan take ake watsi da su.

Kara karanta wannan

'A murƙushe su kawai': Shehi ya faɗi hukuncin Musulunci kan irinsu Bello Turji

Ya ce ya fuskanci tsangwama daga masu cin gajiyar irin waɗancan manufofi (kamar tallafin mai) saboda kawai ya ba da shawarar matakin da ya kamata a ɗauka.

Muhammadu Sanusi II na cikin waɗanda suka ba da shawara ga gwamnatin tarayyya kan cire tallafin mai da wasu matakai da suke ganin sun zama dole don farfaɗo da tattalin arziki.

Sarkin Kano ya ce tun farko ba a saurare su ba.
Muhammadu Sanusi II ya tuna yadda aka yi watsi da shawarwarin da ya bayar Hoto: @masarautarkano
Source: Twitter
“Ba a saurare mu ba, duk wata hujja, duk wata magana mai ma’ana da ta saba wa hanyar da ake bi a wancan lokacin, ba za a ɗauka ba.
"Na fuskanci matsanancin tsangwama saboda ra’ayoyina, don haka ban yi mamakin inda muka tsinci kanmu ba.”

- In ji Khalifa Muhammadu Sanusi II.

Sanusi II ya koka kan naɗa ɓarayi a muƙami

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Buhari II ya koka kan yadda ake naɗa ɓarayi a manyan muƙamai a gwamnatin Najeriya.

Sanusi II ya ce ya zama dole a daina bai wa mutane da suka wawuri dukiyar ƙasa damar sake samun mukaman gwamnati ko damar jagorantar al'umma.

Mai martaba Sarkin ya ce mutane da dama a cikin gwamnati ba su samu tarbiyya ba, shi yasa sukan aikata abubuwa marasa da’a da kima.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262