'Yan Bindiga Sun Titsiye Sarki a Dajin Zamfara, Ya Amsa Tambayoyi Masu Zafi

'Yan Bindiga Sun Titsiye Sarki a Dajin Zamfara, Ya Amsa Tambayoyi Masu Zafi

  • An saki Sarkin Yankuzo, Alhaji Babangida Kogo, bayan Ado Aliero ya tabbatar da bai da hannu a farmakin da aka kai masa
  • ‘Yan bindigar sun yi zargin sarkin ne ya ba sojoji bayanan sirri da suka haddasa kisan ‘yan ta’adda sama da 30 suna bikin aure
  • Rahoto ya nuna cewa babu kudin fansa da aka biya; an ce sun masa tambayoyi na sa’o’i kafin su yarda da cewa bai da alaka da harin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Sarkin Yankuzo da ke karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, Alhaji Babangida Kogo, ya kubuta daga hannun ‘yan bindiga bayan wasu sa’o’i da suka yi suna tambayarsa.

An sace sarkin ne a ranar Talata yayin da yake tserewa daga yankin sakamakon luguden wuta da jiragen saman soji suka yi a dajin da ke tsakanin Yankuzo da Munhaye.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Bam ya tarwatsa yara 3 suna tsaka da wasa a Borno

'Yan bindiga sun saki Sarkin da suka sace a Zamfara
'Yan bindiga sun saki Sarkin da suka sace a Zamfara. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka saki Sarkin ne a wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan an sako shi, ya koma fadarsa a ranar Alhamis, inda ya hadu da iyalansa cikin farin ciki da godiya ga Allah.

Meyasa Ado Aliero ya kama Sarkin?

Rahotanni sun bayyana cewa gungun ‘yan bindigar Ado Aliero ne suka sace sarkin, suna zarginsa da cewa ya bai wa sojoji bayanai da suka kai ga harin da ya hallaka ‘yan ta’adda da dama.

Harin da rundunar Operation Hadarin Daji ta kai ya kashe akalla 'yan bindiga 30, ciki har da shugabanni da dama na gungun, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Wasu majiyoyi sun ce:

“Sun yi zargin cewa shi ne ya ba da sirrin inda suke, amma daga bisani suka tabbatar da cewa bai da hannu.”

An saki Sarki ba tare da kudin fansa ba

Sarkin ya kwashe sa'o'i da dama a hannun ‘yan bindigar kafin suka yanke shawarar sakin sa, bayan sun tabbatar da cewa bai da alaka da harin soji.

Kara karanta wannan

'A murƙushe su kawai': Shehi ya faɗi hukuncin Musulunci kan irinsu Bello Turji

Wani da ke da masaniya da lamarin ya ce:

“Ba a biya ko sisi ba. Sun tambaye shi sosai kafin su gane cewa ba shi ne ya tona sirrin su ba.”

Wannan ya kara bayyana cewa harin da aka kai ya shafi gungun da ke shirin biki ko wata liyafa a dajin da ke kusa da Yankuzo.

Dan bindiga Ado Aliero da ake nema ido rufe
Dan bindiga Ado Aliero da ake nema ido rufe. Imrana Muhammad
Source: Twitter

Ado Aliero na da hannu a harin sojoji

Daily Post ta wallafa cewa bincike ya nuna cewa gungun Ado Aliero ne suka kuma yi kwantan bauna ga sojojin Najeriya a makon da ya gabata.

Ado Aliero na daga cikin mafiya haɗari a cikin masu garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yamma, kuma ana danganta shi da hare-hare da dama da suka haddasa asarar rayuka.

An kama shugaban 'yan ta'addan Mahmuda

A wani rahoton, kun ji cewa ana rade radin jami'an hukumar DSS sun yi nasarar kama shugaban 'yan ta'addan Mahmuda.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama a jihohin Kwara da Neja sun yi farin ciki da jin labarin.

A kwanakin baya 'yan kungiyar Mahmudu suka bayyana a wasu jihohin Najeriya kuma suka rika muzgunawa al'umma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng