Mahaifin Matashi Ɗan Gwagwarmaya da Aka fi Sani da Ɗan Bello Ya Rasu
- Rahotanni sun tabbatar da rasuwar mahaifin Dr. Bello Galadanci, wanda ya rasu a yau Alhamis 7 ga watan Agusta, 2025
- Lauya, kuma daya daga cikin abokan Dan Bello, Abba Hikima shi ya tabbatar da labarin rasuwar a kafar sadarwa a yau Alhamis
- Har yanzu ba a bayyana musabbabin rasuwar ba, sai dai majiyoyi sun ce dattijon ya rasu bayan fama da rashin lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa mahaifin Dr. Bello Galadanci ya riga mu gidan gaskiya.
Ba a bayyana dalilin rasuwar mahaifin Ɗan Bello ba amma majiyoyi sun ce marigayi ya rasu bayan fama da jinya.

Source: Facebook
Daya daga cikin abokan Dan Bello kuma lauya, Abba Hikima shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 7 ga watan Agustan 2025 a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Bello Turji ya saki sabon bidiyo kan sulhu, ya kira babban malami da 'ɓarawo'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gudunmawar Dan Bello wurin kawo sauyi a Najeriya
Dan Bello ya kasance dan gwagwarmaya wanda ba shi da tsoro da ake ganin na daga cikin matasa da za su iya kawo sauyi a kasa.
Yana daga cikin matasan da ke tafiyar matasa wadanda ke ganin idan ba su kalubalanci shugabannin yanzu ba babu wani sauyi da za a samu.
Matashin ya sha kalubalantar gwamnonin jihohi kan sakaci da bangaren ruwan sha, ilimi da kuma harkokin lafiya domin zaburar da su kan abin da ya kamata.

Source: Facebook
Yadda Dan Bello ya taso gwamnoni a gaba
Daga cikin wadanda ya fi sanyawa a gaba su ne gwamnonin Arewa da suka hada da jihohin Kano, Gombe, Borno, Bauchi da sauransu.
Ko a kwanakin nan ma Dan Bello ya dura kan Gwamna Abba Kabir na Kano musamman kan harkar ilimi inda ya je wasu makarantu da suka lalace da ke buƙatar gyara.
Fitar da bidiyon ke da wuya, Gwamna Abba Kabir ya kai ziyarar bazata makarantar tare da ba da umarnin daukar matakin da ya dace.
Hikima ya sanar da rasuwar mahaifin Dan Bello
A cikin sanarwar, Abba Hikima ya ce dattijon ya rasu ne a yau Alhamis 7 ga watan Agustan shekarar 2025.
Lauya Hikima ya yi rubutun kamar haka:
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.
"Allah ya yiwa mahaifin Dr Bello Galadanchi (Dan Bello) rasuwa yanzun nan.
"Allah ya gafarta masa. Ameen."
Legit Hausa ta samu labari cewa tun kimanin karfe 5:00 na yammacin yau Alhamis aka fara yada labarin rasuwar dattijon a zauren WhatsApp.
Daga cikin 'Ya 'yan da ya bari akwai Bello wanda ya shahara da Dan Bello, Irfan da Ihsani Galadanci.
Mutane da dama sun bayyana jimaminsu kan rashin da matashin ya yi inda suka yi ta addu'ar Ubangiji ya yi masa rahama ya kuma saka masa da gidan aljanna.
Dan Bello ya magantu bayan kama shi
A baya, mun ba ku labarin cewa bayan jami’an DSS sun kama Ɗan Bello a filin jirgin sama na Kano, mutane sun yi ta sukar matakin jami'an tsaro.
A cewar Ɗan Bello, jami’an sun karɓi fasfonsa da kayansa kafin su tafi da shi, amma daga baya suka sake shi bayan wani lokaci.
Dan Bello ya ce bai yi mamakin kame shi ba, yana kira ga jama’a da su kwantar da hankali, yana cikin koshin lafiya babu wata matsala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

