Shiri Ya Baci: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna, an Samu Asarar Rayuka
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun shirya mugun nufi kan dakarun sojoji masu aikin samar da tsaro a jihar Katsina
- Miyagun sun yi wa sojoji kwanton bauna bayan motarsu ta lalace cikin daji a karamar hukumar Sabuwa
- Harin da 'yan bindigan suka kai ya jawo asarar rai tare da jikkata wasu sojoji wanda hakan ya jefa rayuwarsu cikin hatsari
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai harin kwanton bauna kan wata mota mai sulke ta sojoji (APC) a cikin dajin Yadi, kusa da kauyen Machika, da ke ƙaramar hukumar Sabuwa a jihar Katsina,
A sakamakon harin wanda 'yan bindigan suka kai a ranar Laraba, an kashe soja guda ɗaya, yayin da wasu biyu suka samu raunuka sosai.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna
Rahotanni sun bayyana cewa motar APC ɗin ta samu matsalar inji ne a yayin da take sintiri a yankin, kafin ‘yan bindigan su kai harin da misalin ƙarfe 2:32 na rana.
Wannan matsala da motar ta fuskanta ya ba 'yan bindigan damar shirya farmaki a kan sojojin da ke cikin ta.
"A lokacin harin, soja guda ya rasa ransa sakamakon harbin bindiga, yayin da wasu biyu suka samu raunin da ke barazana ga rayuwarsu. Nan take aka kwashe su zuwa asibiti domin ba su kulawar gaggawa."
- Wata majiya
Jami'an tsaro sun dauki matakai
Bayan aukuwar lamarin, jami’an tsaro sun tashi da gaggawa domin ɗaukar mataki. An tura jirgin yaki na rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) zuwa yankin domin taimakawa.
Hakazalika, dakarun rundunar Operation Fansan Yanma sun mamaye dajin Yadi domin farauto ‘yan bindigan da suka kai harin.
A halin yanzu, ana ci gaba da tsaurara tsaro a yankin domin bin sawun ‘yan bindigan da kuma kama su domin su fuskanci hukunci.

Source: Original
Hukumomin tsaro sun ce za su ci gaba da matsa lamba a kan masu aikata laifuffuka, tare da tabbatar da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummar da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda a yankin.
Hukumomin suna kuma roƙon jama’a da su bayar da bayanai masu amfani, musamman idan sun ga wani motsi da ya dace a bincika, domin taimaka wa jami’an tsaro wajen ganin an kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a Katsina da Najeriya gaba ɗaya.
Ana rayuwa cikin fargaba
Wani mazaunin jihar Katsina, Sanusi Abubakar, ya shaidawa Legit Hausa cewa mutane na rayuwa cikin fargaba sakamakon tsoron harin 'yan bindiga.
"Hankulanmu kullum a tashe suke saboda fargabar kawo hari. Muna rokon Allah ya kawo mana karshen wannan bala'in."
"Su kuma jami'an tsaro muna addu'ar Allah ya ci gaba da ba su nasara a kan miyagun mutanen nan."
- Sanusi Abubakar
Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina

Kara karanta wannan
Sojojin saman Najeriya sun yi ruwan wuta a garin Raan, an rasa rayukan ƴan bindiga 30
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin 'yan bindiga a jihar Katsina.
Sojojin sun kai daukin gaggawa bayan sun samu rahoton 'yan bindiga na shirin kai wani hari a karamar hukumar Malumfashi.
Jami'an tsaron wadanda suka hada har da 'yan sanda da 'yan sa-kai sun yi nasarar fatattakar 'yan bindigan inda suka kashe daya daga cikinsu tare da kwato makamai
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

