Ana Batun Sulhu da Bello Turji, Ƴan Bindiga Sun Taso Garuruwa 35 a Jihar Zamfara
- Ƴan bindiga sun karbi N800,000 daga kowane kauye daga cikin ƙauyuka 35 da ke ƙarƙashin hakimin Ɗan Isa, ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Zamfara
- Hakimin Ɗan Isa, Malam Hassan Yarima ya tabbatar da hakan, ya ce sai da suka karɓi kudin sannan suka bar manoma suka fara zuwa gona
- Ya ce idan Allah ya kaimu aka gama noman daminar bana, ƴan bindigar sun nemi a ƙara masu makamancin wannan kudi, jimulla N56m kenan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Manoma a yankin Dan Isa da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara sun bayyana cewa ƴan bindiga sun yi musu barazana a wannan lokaci na damina.
Wannan barazana na zuwa ne a daidai lokacin da ake yaɗa labarin cewa ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji, ya ajiye makamai, ya rungumi zaman lafiya.

Kara karanta wannan
'Yan ta'adda sun yi garkuwa da basaraken Zamfara yana tsaka da ƙoƙarin barin gari

Source: Twitter
Amma hakimin Ɗan Isa, Malam Hassan Yarima, ya shaidawa Daily Trust ta wayar tarho cewa kauyukan da ke ƙarƙashinsa na fuskantar barazana daga ƴan bindiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun taso mutanen yankin Ɗan Isa
Hakimin ya ce kowane ƙauye daga cikin ƙauyuka 35 da ke ƙarƙashin gundumarsa ya biya N800,000 kafin mazauna su samu damar fara noman daminar bana.
“Kowanne kauye zai sake biyan N800,000 kafin a bar manoma su girbi amfanin gonarsu. Wannan ne yarjejeniyar da muka cimma da shugaban dabar ƴan bindiga na wannan yankin da ake kira Dan Sadiya."
“Ina magana ne kawai kan yankina, ban san abin da sauran yankuna suka biya ba a wannan shekarar. Amma abin da na sani tabbas shi ne, ba a bar kowa ya fara noma ba sai an biya kuɗi.”
"Ba mu da wani zaɓi face bin umarninsa. Idan ba haka ba, ƴan bindiga ba za su bar mu mu shiga gonakinmu ba. Aƙalla idan mun noma, za mu samu abin ciyar da iyalanmu.”
- In ji Malam Hassan Yarima.
Yadda ƴan bindiga suka matsawa jama'a a Zamfara
Sai dai, Malam Yarima ya koka cewa duk da biyan wannan kuɗi, har yanzu ƴan bindigar na kai musu hari, inda suke sata da sace dabbobi da kayan abinci.
Ya nuna damuwa cewa mazauna yankunan da abin ya shafa sun yi amfani da duk wani abu da ke hannunsu domin neman zaman lafiya da ƴan bindigar, in ji Daily Post.

Source: Facebook
"Muna son mu zauna lafiya da su, amma gaskiya ne cewa sun kwashe komai namu. Sun sace mana dabbobi, sun ɗauke mana kuɗi, amfanin gona da sauran dukiyoyinmu.”
"Suna zuwa ƙauyukanmu a kowane mako, kuma idan suka zo sai mun tattara kuɗi, abinci da kayan masarufi mun miƙa musu. Wani lokaci, bayan sun karɓi kayan, sai su ɗauki mata su tafi da su,” in ji shi.
Sojoji sun tashi wurin bikin ƴan bindiga
A wani rahoton, kun ji cewa jiragen yakin rundunar sojin saman Najeriya sun kai farmaki wurin bikin auren ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Jiragen sojojin sun samu nasarar hallaka gomman ƴan bindiga a wannan samame da suka kai ranar Talata, 5 ga watan Agusta, 2025.
An ruwaito cewa ragowar yan bindigar da suka tsira sun yi kokarin kwashe gawarwaki da wadanda suka jikkata zuwa kauyen Yankuzo domin neman agaji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

