Borno: Hankula Sun Tashi, an Samu Gawar Mji, Mata da ’Ya’yansu a Wani Yanayi

Borno: Hankula Sun Tashi, an Samu Gawar Mji, Mata da ’Ya’yansu a Wani Yanayi

  • An shiga tashin hanakli da iyalai hudu suka mutu kwatsam a kauyen Chatta da ke Hawul a jihar Borno, lamarin da ya tayar da hankalin jama'a
  • An gano gawarsu ne a cikin daki bayan wani dan uwansu ya ziyarci gidan da safe, ya tarar da shiru a gidan kamar ba kowa
  • Ana zargin guba ko hayakin janareto ne ya yi sanadin mutuwar; hukumomi sun fara bincike kan lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Mutuwar bazata ta wasu iyalai hudu a kauyen Chatta da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno ta jefa al’umma cikin alhini da rudani.

Wadanda suka rasu sun hada da Yakubu Samanja, matarsa mai suna Esther Yakubu, da kuma ‘ya’yansu Amos da Maryamu Yakubu.

An samu gawar miji, mata da yayansu a cikin gida
Samun gawar miji, mata da yayansu 2 ya tayar da hankula a Borno. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka tsanci gawar miji, mata da yayansu

Kara karanta wannan

Ministoci, tsohon ɗan majalisa da mutum 5 sun mutu a mummunan hatsarin jirgin sama a Ghana

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce abin ya daga hankulan mutanen yankin a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani dan uwan mamatan mai suna Ibrahim Samanja shi ya fara tabbatar da faruwar lamarin bayan ya kai ziyara a gidan.

Samanja ya ce ya gano lamarin ne da safiyar ranar Talata 5 ga watan Agustan 2025 lokacin da ya ziyarci gidan.

Ya bayyana cewa ya isa gidan da misalin karfe 7:00 na safe, ya buga ƙofa sau da dama, amma ba wanda ya amsa.

Saboda damuwa da shakku da ya shiga, sai ya bude ƙofar da karfi, inda ya tarar mijin da matar da yayansu kwance cikin daki sun mutu gaba daya.

Hankula sun tashi bayan samun gawar miji da mata a Borno
Yan sanda sun fara binciken samun gawar miji, mata da yayansu 2 a Borno. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Borno: Yan sanda sun fara binciken gawarwakin

Bayan faruwar hakan, jami’an ‘yan sanda da ma’aikatan lafiya sun shiga gidan, suka tabbatar da mutuwar duka iyalan a cikin gidan.

An dauki gawarwakin ne zuwa babban asibitin Marama, inda aka ajiye su a dakin ajiye gawarwaki don bincike da adanawa.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ba a ga wata alamar rashin lafiya ko wani matsala a jikin iyalan ba ko kuma alamar kai musu hari kafin mutuwar

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gini ya rufta kan uwa da ƴaƴanta 5 a Katsina bayan mamakon ruwa

Rahotannin farko sun nuna babu alamun tashin hankali a jikin su ko kuma wani hari da aka kai musu, amma ana zargin guba ko hayakin janareto.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a kai ga samun musabbabin mutuwar iyalan ba saboda babu wani alama da zai tabbatar da hakan.

Hukumomi sun fara bincike a hukumance domin gano musabbabin ainihin mutuwar da ta girgiza al’umma da dama.

Gini ya rufta kan uwa, 'ya'yanta a Katsina

Mun ba ku labarin cewa wata uwa da ’ya’yanta biyar sun mutu sakamakon gini da ya rufta kansu a garin Dankama da ke jihar Katsina.

An ce bangon gidan ya rufta kan mutane 10 a cikin gidan da misalin ƙarfe 2:00 na dare, bayan saukar mamakon ruwan sama da aka dauki lokaci mai tsawo ana yi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen da abin ya rutsa da su sun rasu ne suna tsakiyar barci, bayan bangon gidan ya fado a kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.