Akwai Matsala: Gwamnatin Tarayya Ta Kori Ma'aikata, Ta Tilasta wa Wasu Ajiye Aiki a Najeriya

Akwai Matsala: Gwamnatin Tarayya Ta Kori Ma'aikata, Ta Tilasta wa Wasu Ajiye Aiki a Najeriya

  • Gwamnatin Tarayya ta sallami jami'ai 15 na hukumar gidajen gyaran hali ta ƙasa (NCoS) tare da ragewa wasu ma'aikata 59 girma
  • A wata sanarwa da kakakin hukumar, Umar Abubakar ya fitar, ya ce an ɗauki wannan matakin saboda jami'an sun aikata laifuffuka da rashin ɗa'a
  • Ya ce ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, hukumar za ta tabbatar da cewa jami'anta na bin ƙa'idoji

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta kori ma’aikata 15 na Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS) tare da rage matsayin wasu 59 saboda aikata laifuffuka da rashin da’a a wurin aiki.

Wannan na cikin sanarwar da Hukumar CDCFIB, mai kula da harkokin hukumar tsaron fararen hula, gyaran hali, kwana-kwana da shige da fice ta fitar.

Shugaban NCoS, Nwakuche Ndidi
Jami'an hukumar gyaran hali 15 sun rasa ayyukansu bayan kama su da laifi Hoto: @CorrectionsNG
Source: Twitter

Sanarwar ta ce an ɗauki wannan matakin ne bayan nazari kan hukuncin ladabtarwa da suka shafi jami’an hukumar daga sassa daban-daban na ƙasar, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Rashin imani: An shiga wurin da ake bauta, an kashe mutumi ɗan shekara 45

Me yasa gwamnati ta kori ma'aikata 15?

A cewar Umar Abubakar, jami’in hulɗa da jama’a na NCoS, hukuncin ya biyo bayan shawarwarin da kwamitin ladabtarwa da manyan ayyuka (BDGPC) ya bayar, bayan bincike mai zurfi.

Ya ce wannan mataki ya ƙara nuna ƙudurin gwamnatin tarayya na tabbatar da da’a da biyayya a cikin hukumar gyaran hali.

“Bayan cikakken nazari da dubawa, hukumar ta amince da ɗaukar matakan ladabtarwa daban-daban domin tabbatar da da’a da kiyaye mutuncinta.
“An kori ma’aikata 15 gaba ɗaya saboda manyan laifuffuka da karya ƙa’idar aiki. An rage matsayin ma’aikata 59 saboda tabbatar da sabawa ƙa’idar aiki da rashin da’a. Sannan an tura wasiƙun gargadi ga ma’aikata 42."

- Umar Abubakar.

An tilastawa wasu jami'an NCoS ajiye aiki

Har ila yau, Umar Abubakar ya ce an wanke ma’aikata 16 daga zarge-zargen da ake musu, yayin da wasu bakwai ke kan dakatarwa domin tantance hannunsu a wani laifi da ake bincike.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun yi garkuwa da basaraken Zamfara yana tsaka da ƙoƙarin barin gari

A rahoton PR Nigeria, Umar ya ƙara da cewa:

“Bayan haka an dakatar da jami’i daga aiki tare da bayar da umarni a miƙa shi ga Hukumar EFCC domin gurfanar da shi a gaban kotu saboda girman laifin da ya aikata.
"Ma’aikata 8 an tilasta musu yin ritaya yayin da aka dawo da jami’i ɗaya kan tsohon matsayinsa, tare da umarnin ya mayar da albashin da ya karɓa lokacin da yake rike da sabon matsayin da ya samu ba bisa ƙa'ida ba.
Jami'an hukumar gyaran hali.
Gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin ladabtarwa kan wasu jami'an NCoS da suka aikata laifi Hoto: @CorrectionsNG
Source: Twitter

A ƙarshe, Umar ya ce hukumar CDCFIB, ƙarƙashin Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, na nan kan bakarta na tabbatar da bin ƙa'idoji a tsakanin ma'aikata.

Gwamnatin Tarayya za ta ɗauki ma'aikata 30,000

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta buɗe shafin daukar sababbin ma’aikata a hukumomi hudu da ke ƙarƙashin ma'aikatar cikin gida.

Za a dauki ma'aikata ne a hukumar shige da fice, hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC, hukumar kashe gobara, da kuma hukumar gidajen gyaran hali.

An shirya fara ɗaukar aikin tun a ranar 26 ga Yuni, amma daga bisani aka dage zuwa yau Litinin , 14 ga Yuli 2025 saboda wasu dalilai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262