Daliban Yobe Sun Samu Tagomashi, Gidauniyar Atiku Ta Dauki Nauyin Karatunsu
- Gidauniyar Atiku Abubakar ta ba Nafisa Abdullahi, Rukaiya Fema da Khadija Kalli cikakken tallafin karatu daga sakandare har jami’a
- Ta bayyana cewa an ba daliban dama su yi karatu kyauta a duk wata makaranta da suka zaɓa, saboda bajintar da suka nuna a gasar TeenEagle
- Atiku ya taya daliban murna, yana mai bayyana Nafisa a matsayin abin koyi ga sauran dalibai da nuna hazakar da aka da ita a Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Yobe – Gidauniyar Atiku Abubakar (AAF) ta ba da cikakken tallafin karatu ga daliban Yobe uku da su ka fito da martabar Najeriya a daraussan Turanci a Landan.
Nafisa Abdullahi, Rukaiya Fema, da Khadija Kalli sun nuna bajinta da suka nuna a gasar TeenEagle Global Finals da aka kammala kwanan nan.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya ba iyalan 'yan wasan kano da su ka rasu tallafin miliyoyin Naira da filaye

Source: Facebook
A takardar da Umar Yobe ya wallafa a shafin Facebook, gidauniyar ta nuna jin dadi a kan yadda daliban sun lashe gasar ne a tsakanin takwarorinsu daga sassa shida na duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gidauniyar Atiku ta dauki nauyin karatun ɗalibai
Jaridar Punch ta wallafa cewa tallafin na kunshe a wata wasiƙa mai kwanan watan 5 ga Agusta, 2025, Farfesa Ahmadu Shehu, mukaddashin sakataren gidauniyar ya sanya wa hannu.
A cikin wasiƙar, gidauniyar ta jinjina wa ƙoƙarin da ‘yan matan suka yi, tana mai tabbatar da cewa tallafin zai ɗauki bauyin duk kuɗin karatunsu daga matakin sakandare har zuwa jami’a, a kowace makaranta da suka zaɓa.

Source: Twitter
Nafisa Abdullahi mai shekara 17 ta fi fice a gasar saboda ƙwarewarta a harshen Turanci, basirar nazari da muhawara, inda ta doke ‘yan wasa daga nahiyoyi shida.
A wata sanarwa da Atiku ya fitar ranar Laraba, ya taya Nafisa murna bisa nuna ƙwarewa a harshen Turanci a duniya.
Ya ce:
“Nasarar da kika samu shaida ce ta hazakarki."
Atiku ya yaba wa dalibar Yobe
Gidauniyar ta sake jaddada kudirinta na tallafawa ilimi mai inganci, musamman ga mata da waɗanda ke cikin barazanar samun karancin ilimi.
Ta ce:
“A matsayinmu na gidauniyar da ke da alhakin tsara ayyukan jin kai na Alhaji Atiku Abubakar, GCON – wanda aka sani da jajircewarsa ga inganta ilimi a Najeriya – mun ƙuduri ci gaba da tallafawa ilimi, musamman ga ‘yan mata da mabukata.”
Tun da farko, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da shirya bikin musamman domin girmama waɗannan matasa saboda yadda suka ɗaukaka jihar da ƙasar Najeriya gaba ɗaya.
A cewarsa:
“Wannan gagarumar nasara abin alfahari nc, kuma shaida ce cewa inganta fannin ilimi na da amfani matuƙa.”
An gwangwaje daliban Yobe da kyaututtuka
A wani labarin, kun ji cewa fitaccen mai rajin ci gaban al’umma, Alhaji Kashim Tumsah, ya ba da tallafin kuɗi na Naira miliyan 1.5 da sababbin kwamfutoci ga ɗalibai uku daga jihar Yobe.
Daliban uku sun nuna bajinta, inda su ka doke fiye da mutum 20,000 daga ƙasashe 69, har su ka zama zakaran gwajin dafi a bangarori daban daban da su ka shafi darussan turanci.
Tumsah ya danganta wannan nasara da jajircewar gwamnatin Yobe karkashin Gwamna Mai Mala Buni wajen saka jari a ilimi da inganta muhalli mai kyau ga koyo da koyarwa.
Asali: Legit.ng

