Lokaci Ya Yi: Babban Mai Ɗauko Rahoto ga Gwamnan Kano, Sadiq Gentle Ya Rasu
- Wani babban mai ɗauko rahoto ga gwamnan Kano, Sadiq Gentle ya rasu bayan jinyar raunukan da aka masa a asibitin Murtala
- Tun farko dai wasu ɓata gari da ba a gano ko su waye ba har kawo yanzu sun farmaki Sadiq Gentle har gida, suka caccaka masa wuƙa a jiki
- Mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya je har asibitin ya duba lafiyarsa kafin Allah ya masa rasuwa yau Alhamis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Babban mai ɗauko rahoto ga gwamnan jihar Kano (SSR), Sadiq Gentle ya riga mu gidan gaskiya bayan fama jinyan raunukan da aka yi masa.
Sadiq Gentle, wanda ke ɗauko wa Gwamna Abba Kabir Yusuf rahoto a ma'aikatar kula da harkokin tarihi da al'adu ya rasu ne a asibiti yau Alhamis, 7 ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya ba iyalan 'yan wasan kano da su ka rasu tallafin miliyoyin Naira da filaye

Source: Facebook
Jaridar Leadership Hausa ta tattaro cewa Sadiq Gentle ya rasu ne sakamakon munanan raunukan da wasu ɓata gari suka ji masa da adduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka faramaki Sadiq Gentle a Kano
Tun farko dai, rahotanni sun nuna cewa wasu ƴan daba sun farmaki matashin har cikin gida, suka sassare shi tare burma masa wuƙa a wurare daban-daban a jikinsa.
Hakan ya sa aka garzaya da shi asibitin Murtala da ke cikin birnin Kano domin kula da lafiyarsa.
Wannan al'amari ya tayar da hankulan mutanen Kano ganin yadda ƴan daba ke iya zuwa har gida su aikata irin wannan ta'adi.
Sarki Sanusi II ya duba lafiyar Sadiq Gentle
Mai martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammad Sanusi II , ya kai ziyara asibitin domin duba jikin Sadiq Gentle saboda yana ɗaya daga cikin masoyansa.
Masarautar Kano ta tabbatar da zuwan Sanusi II asibitin domin diba jikin Sadiq a wata gajeruwar sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba, 6 ga Agusta. 2025.
Allah ya yiwa Sadiq Gentle rasuwa bayan jinya
Kwana ɗaya bayan zuwa Sarki Muhammadu Sanusi II, Allah ya karɓi rayuwar babban mai ɗauko rahoto ga gwamnan Kano, Sadiq Gentle.
Wannan rasuwa ta ja hankali mutanen Kano, inda wasu ke nuna baƙin cikinsu kan aika-aikar da aka yi masa wanda ya yi sanadiyyar rasuwarsa.
Wani Hon. Isah Umar ya nuna damuwarsa a shafin X, ya ce:
"SSR na Gwamnan Jihar Kano Hon. Sadiq Gentle dai ya rasu, Wadanda da aka tura har gida su kashe shi buri ya cika, Allah gaka gasu nan.
"Allah duk masu hannu a wannan kisan Allah ka wulaƙanta su Allah Ka ɗora musu musibah tun daga nan duniya."
An kama babban ɗan daba a jihar Kano
A wani labarin, kun ji cewa ƴan sanda sun yi nasarar kama ɗaya daga cikin manyan ƴan dabar da suka addabi al'ummar Kano, Mu'azu Barga.
Ɗan dabar ya shiga hannu ne a lokacin da ƴan sanɗa suka kai samame wurare daban-daban domin kawo ƙarshen ta'addancin ƴan daba a Kano.
Bincike rundunar ya nuna cewa Barga na daga cikin waɗanda ke jagorantar hare-haren ‘yan fashi da tashe-tashen hankula a cikin birnin Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
