Gwamna Abba Ya ba Iyalan 'Yan Wasan Kano da Su ka Rasu Tallafin Miliyoyin Naira da Filaye
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da tallafi ga iyalan 'yan wasa 22 na Kano da suka rasu a hadarin mota yayin dawowa daga gasa a jihar Osun
- Gwamnati ta bayyana cewa an samu tallafin daga Remi Tinubu, gwamnatin Ogun, Injiniya Sagir Ibrahim Koki da kungiyar kwallon raga
- Baya ga iyalan wadanda suka rasu, gwamnatin Abba ta kuma muka tallafin kudi da filaye ga 'yan tawagar da su ka samu raunuka
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa iyalan 'yan wasa 22 na Kano da suka rasu a mummunan haɗarin mota da ya faru ranar 31 ga Mayu, 2025, tallafin kuɗi ₦5,000,000 da filaye.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗannan 'yan wasa na dawowa daga gasar National Sports Festival da aka gudanar a jihar Ogun ne lokacin da haɗarin ya rutsa da su.

Source: Facebook
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam, ya fitar kuma ya wallafa a shafinsa Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya gana da iyalan 'yan wasan Kano
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kwamishinan Matasa da Wasanni ya bayyana wannan lamari yayin taron majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Kwankwasiyya city.
A lokacin taron, Gwamna Abba ya dakatar da zaman domin karɓar iyalan 'yan wasan tare da jajanta masu bisa iftila'in.
Ibrahim Adam ya ce gwamnan ya bayyana ‘yan wasan da suka rasu a matsayin 'Jaruman Kano' tare da nanata kudirin gwamnatinsa na girmama su da tarihin da suka bari.
A cewarsa:
“Gwamnan ya saurari korafin iyalan cikin tausayi kuma ya bayar da umarnin a raba duk wata gudummawa da aka tara ba tare da ɓata lokaci ba.”

Source: Facebook
Wadanda suka ba da tallafin sun hada da Remi Bola Tinubu N110,000,000m, gwamnatin jihar Ogun N32,000,000, Injiniya Sagir Ibrahim Koki N2,200,000m, da kungiyar kwalon raga sun ba da 500,000 .
Mutanen da suka samu tallafin Gwamnan Kano
A cewar Ibrahim Adam, jimillar tallafin da kowane iyali ya samu ya kai ₦11,709,375 da fili, yayin da kowanne daga cikin waɗanda suka tsira da raunuka za su samu ₦3,709,375 da fili.
Ibrahim ya ce:
“Wannan hali na jin kai da jagoranci da Gwamna Yusuf ya nuna ya jawo yabo daga mutane da dama a fadin jihar Kano, kuma yana nuna jajircewar gwamnatinsa wajen kula da jin daɗin jama'a.”
Gwamnan ya kuma kammala zaman da addu’a ga mamatan da kuma godiya ga dukkanin masu bada gudummawa.
“Allah ya saka da alheri ga duk wanda ya ba da tallafi, ya kuma jikan jaruman 'yan wasanmu da rahama,” in ji Gwamna Yusuf ta bakin Ibrahim Adam.
Baya ga gudummawar da aka tara daga jama'a, Gwamna Abba ya ƙara bayar da ₦5,000,000 da fili ga kowane iyali daga cikin iyalan da suka rasa ɗan uwansu.
Sannan waɗanda suka tsira da raunuka za su samu ₦2,000,000 da fili kowannensu daga gwamnatin jihar Kano.
Ibrahim Adam ya jaddada cewa:
“Wannan tallafi daga Gwamna Yusuf alama ce cewa gwamnatinsa ba za ta manta da waɗannan iyalai ba.”
'Yan wasan Kano sun rasu a hadari
A baya, mun wallafa cewa akalla ’yan wasa da jami’ai 21 daga Kano da suka wakilci jihar a gasar wasanni ta kasa da aka kammala a jihar Ogun sun rasa rayukansu.
Hatsarin ya auku ne da misalin 8:00 na safe a ranar Asabar, 31 ga watan Mayu, 2025, a gadar Daka Tsalle da ke ƙaramar hukumar Garun Malam suna dab da shigo wa Kano.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sama da mutum 10 sun jikkata sosai, yayin da wasu suka rasu nan take a wurin da hatsarin ya faru, lamarin da ya jawo takaici a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


