Hako Fetur a Arewa: Bayan Kolmani, Jihar Kogi Ta Fara Shirin Tono Danyen Mai
- Gwamnatin jihar Kogi ta fara kokarin shawo kan masu zuba jari don fara hakar danyen mai da iskar gas a jihar
- Gwamna Ododo ya gana da Ministan albarkatun mai da shugaban hukumar NUPRC domin hakar mai a jihar Kogi
- Kogi ta zama daga cikin jihohin Arewa da gwamnatin tarayya ta tabbatar da samuwar danyen mai a cikinta a 2022
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta fara daukar matakan jawo masu zuba jari domin gudanar da hakar danyen mai da iskar gas a fadin jihar.
Wannan na zuwa ne bayan ganawa da aka yi da Gwamna Ahmed Usman Ododo, ministan albarkatun mai, Heineken Lokpobiri, tare da shugaban hukumar NUPRC, Gbenga Komolafe.

Source: Facebook
Tashar NTA ta wallafa a X cewa ganawar ta gudana ne a hedikwatar ma’aikatar albarkatun mai da ke Abuja.

Kara karanta wannan
Tinubu: Gwamnati ta kashe N26.38bn a kan jiragen shugaban ƙasa a cikin watanni 18
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga haka, ta mayar da hankali kan hanyoyin da za a bi don jawo masu zuba jari domin ciyar da aikin hakar albarkatun man fetur gaba a jihar Kogi.
Jihar Kogi na shirin hako danyen mai
Ododo ya bayyana shirye-shiryen jiharsa na hadin gwiwa da hukumomin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki wajen amfani da albarkatun kasa domin kara habaka tattalin arziki.
Ya ce gwamnati ta dauki matakai masu muhimmanci kamar kafa hukumar raya yankunan da ake hako mai a jihar domin tabbatar da cewa jama'a da masu zuba jari sun amfana da ci gaban.
Gwamnan ya ce tun a watan Oktoban 2024 ya bayyana kudirin gwamnatin jihar Kogi na samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari domin gudanar da aikin hakar mai cikin lumana.

Source: Facebook
NNPCL na goyon bayan hakar mai a Kogi
Tashar TVC ta wallafa cewa ministan albarkatun mai, Sanata Lokpobiri, ya bayyana jihar Kogi a matsayin daya daga cikin jihohin da suke da arzikin mai a Najeriya.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da goyon bayan jihar wajen jawo masu zuba jari da bunkasa aikin hakar albarkatun man da ke cikin ta.
A cewarsa, bisa tanadin dokar harkar man fetur ta 2021, an ba hukumar NUPRC damar amfani da asusun bunkasa wuraren hakar mai domin gano sababbin rijiyoyin mai a fadin kasar nan.
Hakar mai: Kogi na sahun gaba a Arewa
A shekarar 2022, gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa an gano danyen mai a jihar Kogi a gwargwadon yadda za a iya hako shi.
Wannan ya sa jihar ta zama ta farko farko a yankin Arewa da aka tabbatar da samun albarkatun mai a cikinta.
Ana ganin hakan zai taimaka wa jihar wajen habaka tattalin arzikinta da kara samun kudin shiga na cikin gida.
NNPCL ya cigaba da hako mai a Kolmani
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin NNPLC ya tabbatar da cewa ya cigaba da aikin hako mai a Kolmani.
Wani jami'in NNPCL ne ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce a yanzu haka an tono rijiyoyi hudu a wajen.
Bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna shakku kan cigaba da aikin a gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
