Sauƙi Ya Samu: NNPCL Ya Canza Farashin Litar Fetur Karo na 2 cikin Awanni 48 a Najeriya
- Gidajen man kamfanin NNPCL na ƙasa sun rage farashin kowace litar fetur a babban birnin tarayya Abuja da jihar Legas a jiya Laraba
- An ruwaito cewa kamfanin mai na Najeriya ya sauke farashin lita daga N915 zuwa N875 a jihar Legas, sai kuma daga N955 zuwa N900 a Abuja
- Wannan ragi da kamfanin NNPCL ya yi na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan ƙara farashin litar fetur a biranen guda biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) ya rage farashin litar man fetur a gidajwn mai da ke babban birnin tarayya Abuja da jihar Legas.
Wannan sauƙin na zuwa ne biyo bayan ƙarin farashin da kamfanin NNPCL ya yi kwanaki biyu da suka gabata inda ya ɗaga farashin zuwa N915 a Legas da N955 a Abuja.

Source: Getty Images
A jiya, ranar Laraba, 6 ga Agusta, 2025, jaridar The Cable ta lura cewa gidajen man NNPC sun rage farashin man fetur da aƙalla N40 a kowace lita a Legas da birnin Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ya rage farashin fetur a Najeriya
A jihar Legas, farashin kowace lita ɗaya ya sauka zuwa N875 a gidan man kamfanin NNPCL da ke Fadeyi, yankin unguwar Western Avenue.
Haka nan kuma a gidan man NNPCL da ke cikin ofishin hukumar kula harkokin gidaje (FHA) a Kubwa, Abuja, an sayar da man fetur a farashin N900 kowace lita jiya Laraba.
Sai dai, abokan hulɗar matatar Dangote, wato Mobil da AP sun ci gaba da sayar da man a farashin N915 kowace lita ba tare da sauyi ba.
A ranar 31 ga Yuli, Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa matsakaicin farashin litar fetur ya ƙaru zuwa N1,037.66 a watan Yuni 2025, daga N750.17 da aka sayar a Yuni 2024.
Jihohin da ake samun fetur da tsada/araha
Rahoton ya nuna cewa jihohin Jigawa, Ondo da Legas ne suka fi ko'ina sayan man fetur da tsada a watan Yuni.
A gefe guda, jihohin Yobe, Kogi da Imo ne suka fi araha, inda aka sayar da man a matsakaicin farashin N950.60, N986.67, da N987.86 kowace lita bi-da-bi, in ji NBS.

Source: Getty Images
Wannan ragi da kamfanin NNPCL ya yi na iya kawo sauƙi ga ƴan Najeriya duk da mutane na ganin ko da an sauke farashin litar fetur, ba ya isowa ga talakawa.
Kwastam za ta sayar da fetur a farashi mai rahusa
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar Kwastam ta ƙasa ta samu nasarar kama lita 69,375 na man fetur da gas da aka yi yunkurin fitar da su daga Adamawa da Taraba zuwa ƙasar waje.
Jami’an kwastam na yankin Arewa maso Gabas ne suka samu wannan nasara a cikin mako shida da suka gabata, karkashin shirinsu na yaki da fataucin kaya.
Hukumar Kwastam ta ce za a sayar da jarkunan man da aka kama ga jama’a a kan ₦10,000 bisa umarnin gwamnatin tarayya domin rage radadin matsin tattalin arziki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

