Ana Jiran Tinubu Ya Karrama Daliban Yobe, Lauya Ya Gwangwaje Su da Kyaututtuka

Ana Jiran Tinubu Ya Karrama Daliban Yobe, Lauya Ya Gwangwaje Su da Kyaututtuka

  • Fitaccen ‘dan kasuwa Alhaji Kashim Tumsah ya shiga jerin wadanda suka karrama daliban jihar Yobe da suka fito da Najeriya a idon duniya
  • Tumsah, wanda ya yi fice a rajin kawo ci gaba ya ba su kyautar N1.5m da kwamfutoci, domin yabawa da irin bajintar da su ka yi
  • Ya danganta nasarar da ƙoƙarin gwamnatin Yobe a fannin ilimi, yana mai cewa Gwamna Mai Mala Buni yana kokari sosai wajen inganta ilimi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Fitaccen mai rajin cigaban al’umma, Alhaji Kashim Tumsah, ya bayar da kyautar kuɗi N1.5m ga ɗalibai uku daga Yobe da su ka lashe gasar Turanci da muhawara ta duniya.

Nafisa Abdullahi mai shekara 17, Ruqayya Fema mai shekara 15, da Hadiza Kalli dukkaninsu dalibai ne a makarantar Nigeria Tulip International College da ke Mamudo ne suka wakilci Najeriya a gasar.

Kara karanta wannan

'Najeriya ka iya wargajewa kafin zaɓen 2027': Tsohon minista ya yi hasashe

Daliban Yobe sun yi bajinta
Lauya ya karrama daliban Yobe Hoto: Mamman Muhammad
Source: Facebook

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa waɗannan ɗaliban sun doke mutum 20,000 daga ƙasashe 69 a gasar kuma su ka zama zakaran gwajin dafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaliban Yobe sun yi nasara a gasar Turanci

Legit ta ruwaito cewa Tumsah, wanda lauya ne, ya baiwa kowace ɗaya daga cikin ɗaliban kyautar Naira 500,000 da kuma sabon kwamfuta.

Ya ce:

“Muna alfahari da wannan gagarumar nasara da ɗalibai uku masu hazaka daga Yobe suka samu – Nafisa, Rukayya da Hadiza – waɗanda suka kawo wa Najeriya ɗaukaka a gasar TeenEagle Global English Championship da aka yi a London.”
“Samun nasara a cikin mutum fiye da 20,000 daga ƙasashe 69, ya nuna basirar su da kuma tarbiyyar da suka samu ta fannoni da dama.”

An jinjinawa ɗaliban Yobe da suka ci gasa

Alhaji Tumsah, wanda kuma aka fi sani da KMT, ya danganta nasarar da ɗaliban suka samu da cigaban da ake samu a fannin ilimi ƙarƙashin Gwamna Mai Mala Buni.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kara kamen dilan kwaya a Kano bayan gagarumin samame

Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni
Lauya ya jinjina tsarin ilimin gwamntin Yobe Hoto: Mamman Muhammad
Source: Facebook

Ya ce sadaukarwar gwamnan wajen inganta muhallin koyo da koyar wa jihar na haifar da 'da mai ido.

Ya ce:

“Wannan nasara abin alfahari ce ba kawai ga Yobe ba, har da Najeriya baki ɗaya. Ta kuma zama abin koyi cewa idan an baiwa hazaka dama, abubuwa da dama na iya yiwuwa."

A farkon shekarar nan, Tumsah ya bai wa ɗalibai 29 daga jihar tallafin N100,000 kowanne bayan sun samu maki 300 ko sama da haka a jarabawar UTME ta 2025.

Tinubu ya jinjina wa daliban Yobe

A baya, mun wallafa cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya dalibai mata uku na Najeriya murna bisa gagarumar nasarar da suka samu a gasar TeenEagle ta duniya da aka yi a Landan.

Daliban, wadanda 'yan asalin Yobe ne sun yi nasara a fannoni daban-daban na ilimin harshen Turanci, inda kowaccensu ta lashe babbar lambar yabo saboda bajintar da suka nuna.

Shugaban ya ce wannan nasara ta nuna cewa matasan Najeriya na da irin hazakar da duniya ke nema, kuma idan aka ba su horo da dama, za su ci gaba da kawo wa ƙasa ɗaukaka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng