Rashin Imani: An Shiga Wurin da Ake Bauta, An Kashe Mutumi Ɗan Shekara 45

Rashin Imani: An Shiga Wurin da Ake Bauta, An Kashe Mutumi Ɗan Shekara 45

  • Ana zargin an harbe wani mutumi ɗan kimanin shekara 45 har lahira a cikin coci a yankin karamar hukumar Ukanafun ta jihar Akwa Ibom
  • Rundunar ƴan sanda ta tura jami'ai wurin bayan kisan kuma an gano ƙaramar bindiga ƙirar gida, wacce ake tunani an yi amfani da ita
  • Kwamishinan ƴan sanda na jihar Akwa Ibom ya bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano masu hannu a wannan ɗanyen aiki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Wani mutum mai suna Udeme Sunday Uko, mai shekara 45 da haihuwa ya rasa ransa a wurin ibadar Kiristoci watau coci a jihar Akwa Ibom.

Rahoto ya nuna cewa an harbe mutumin har lahira a cikin wata coci da ke karamar hukumar Ukanafun ta jihar Akwa Ibom da ke Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

An so a tashi gari, ƴan sandan Kaduna sun gano bam aka ɓoye a kayan gwangwan

An kashe wani mutumi a wurin Ibada a Akwa Ibom.
Yan sanda sun dauke gawar wani magidanci da aka harbe a cikin coci a Akwa Ibom
Source: Original

Daily Trust ta ruwaito cewa an samu gawar Sunday Oko cikin jini, bayan ya kwanta barci tare da iyalinsa a cikin cocin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe magidanci a cocin Akwa Ibom

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom, DSP Timfon John, ta ce:

"Rahoton farko ya nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:10 na safiyar Talata, ranar 5 ga watan Agusta, 2025.”
"Mutumin da matarsa da yaransa na kwance suna barci a cikin wata coci da ke kauyen Ikot Oku Usung, lokacin da aka ji harbin bindiga, daga bisani kuma aka gano cewa Mista Uko aka harba a kansa.
"Wannan yana iya nuni da ko dai kisan kai ne ko kuma harin da abokan gaba suka kai masa, bincike ne kaɗai zai bayyana gaskiyar al’amarin.”

Dakarun ƴan sanda sun kai ɗauki cocin

A wata sanarwa da DSP Timfon John ta fitar daga Uyo a ranar Laraba, rundunar ‘yan sanda ta ce wasu mutane ne suka kai rahoton lamarin, bayan samun bayanai daga matar mamacin, rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kara kamen dilan kwaya a Kano bayan gagarumin samame

"Bayan an kawo mana rahoton, nan take dakarun ‘yan sanda suka nufi wurin da abin ya faru. A wajen bincike, an gano ƙaramar bindiga ƙirar gida da ake kyautata zaton da ita aƙa yi amfani.
"An garzaya da gawar mamacin zuwa dakin ajiye gawawwaki don ajiya da kuma binciken likita,” in ji DSP John.
Yan sanda suna fara bincike.
Kwamishinan ƴan sandan Akwa Ibom ya ba da umarnin binciko waɗanda suka yi kisa a coci Hoto: Nigeria Police Force
Source: Getty Images

Yan sanda za su kama duk mai hannu a kisan

Ta kuma bayyana cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, Baba Mohammed Azare, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka aikata kisan.

Kakakin ƴan sanda ta ce rundunar za ta yi duk mai yiwuwa wajen cafke duka masu hannu a wannan ɗanyen aiki domin su girbi abin da suka shuka.

An kashe ango bayan kwana 2 da aure

A wani labarin, kun ji cewa an kashe wani sabon ango da aka ɗaura aurensa a ranar 2 ga watan Agusta, 2025 a jihar Benuwai, an hallaka shi tare da abokinsa.

Rahoto ya nuna cewa an gano gawarwakin waɗanda aka kashe a Ulam, yankin da masu magana da harshen Tiv ke zaune, duk da an san suna zaman lafiya.

Sai dai wani mazaunin Tiv daga Gwer ta Gabas, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya yi ikirarin cewa makiyaya ne suka aikata kisan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262