Shugaban EFCC Ya Kare Kansa kan Batun Tilastawa Ojulari Yin Murabus a NNPCL

Shugaban EFCC Ya Kare Kansa kan Batun Tilastawa Ojulari Yin Murabus a NNPCL

  • Batun tilastawa shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) yin murabus, ya yi yawo sosai a karshen makon da ya gabata
  • Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya fito ya nesanta kansa daga rahotannin da ke cewa ya tilastawa Bayo Ojulari yin murabus
  • Ola Olukoyede ya yi barazanar daukar matakin shari'a idan wadanda suka buga labarin ba su fito sun bayar da hakuri ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya kare kansa kan batun tilastawa shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari, yin murabus.

Ola Olukoyede ya karyata rahotannin da ke cewa ya tilastawa shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, yin murabus.

Shugaban EFCC ya kare kansa kan Bayo Ojulari
Shugaban EFCC ya musanta tilastawa Ojulari yin murabus Hoto: @OfficialEFCC, @nnpclimited
Source: Twitter

Olukoyede ya musanta tilastawa yin Ojulari murabus

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a shafin X ranar Laraba, 6 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

'Dan shekara 32 ya yi barazanar kashe gwamna, ya jefa kansa a babbar matsala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olukoyede ya kalubalanci wani rahoto da wata jaridar yanar gizo ta wallafa, wanda ke zargin cewa ya sace Ojulari tare da tilasta masa yin murabus a Abuja.

Shugaban na EFCC ya bukaci jaridar ta yanar gizo da ta janye rahoton, tare da bayar da hakuri a bainar jama’a cikin awanni 48.

Ko da yake an ruwaito cewa Ojulari ya yi murabus, har yanzu shi da kansa, kamfanin NNPCL, ko fadar shugaban kasa ba su fitar da wata sanarwa ko bayani kan lamarin ba.

A ranar Litinin, duk da rade-radin murabus dinsa, Ojulari ya halarci wani taron kungiyar injiniyoyin man fetur ta kasa a Legas.

Shugaban hukumar EFCC zai dauki mataki

Da yake karyata rahoton cewa ya tilasta Ojulari yin murabus, Olukoyede ya bayyana labarin a matsayin na rashin adalci kuma mai zubar da mutunci.

A jawabin, an ji shugaban kamfanin na NNPCL yana mai cewa hakan yana iya nuna shi tamkar wanda ya ci amanar jama’a da mukaminsa.

Kara karanta wannan

'A bi a sannu,' Jagora a APC ya yi magana kan fara yi wa Tinubu kamfe

Shugaban EFCC ya musanta sace Bayo Ojulari
Shugaban EFCC ya ce bai tilastawa Ojulari yin murabus ba Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Olukoyede ya ce lauyansa, Adeyinka Olumide-Fusika (SAN), ya rubuta takarda zuwa ga jaridar, yana neman ta ba da hakuri tare da janye labarin.

Lauyan ya bukaci jaridar ta gane kuskurenta, ta bayyana cewa duk abin da ta wallafa game da wanda yake karewa ƙarya ne, ta bayar da cikakken hakuri ba tare da wani sharadi ba.

Sannan ta janye labarin daga shafinta na yanar gizo da kuma duk wata kafar sada zumunta da ta wallafa labarin.

Lauyan na Olukoyede ya yi gargaɗin cewa idan jaridar ta kasa bin umarnin, za su gabatar da ƙara a kotu domin kalubalantar batanci da ɓata suna da aka yi wa shugaban EFCC, musamman yadda hakan ke da nasaba da mukaminsa a hukumance.

EFCC ta fara binciken wasu gwamnoni

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar yaki da cin hanci ta EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa aun fara bincikar wasu gwamnoni.

Kara karanta wannan

Ojulari: Shugaban NNPCL ya kawo karshen jita jita kan batun murabus dinsa

Ola Olukoyede ya bayyana cewa akwai gwamnoni 19 da hukumar ta fara bincike kansu kan zargin aikata ba daidai ba.

Shugaban na EFCC ya bayyana cewa da zarar wadannan gwamnonin sun sauka daga kan mulki, za a shiga mataki na gaba a binciken.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel