Masoyan Pantami Sun Dura kan Shehi da Ya ce Malam Bai Gina Masallaci Ko 1 ba
- Ana zargin cewa Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe ya soki tsohon minista, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a jihar Gombe
- Albaniy ya nuna Pantami bai tallafawa limamai ko ladanai ba lokacin da yake minista, yana mai zargin rashin taimako ga addini
- Masoyan Pantami sun kare shi, suna cewa ya gina masallaci a makarantar sakandare a birnin Gombe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Kalaman Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe kan Farfesa Isa Ali Pantami sun jawo ce-ce-ku-ce.
Sheikh Albaniy Gombe ya yi magana ne kan tsohon ministan inda ya sakaye sunansa yana maganar bai gina masallaci ko daya ba a Gombe.

Source: Facebook
Sheikh Albaniy ya soki Farfesa Pantami a Gombe
Hakan na cikin wani faifan bidiyo mai tsawon minti 1:09 da malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Laraba 6 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan
A karshe, Tinubu ya magantu game da 'yan Yobe da suka lashe gasar Turanci a London
Duk da malamin bai ambaci suna ba a faifan bidiyon, wakilin Legit Hausa ya tuntubi na kusa da shi inda ya tabbatar da Farfesa Pantami yake.
Malam Muhammad Rabiu ya ce tabbas da Farfesa Pantami yake inda ya tabbatar da cewa abin da Sheikh Albaniy ya fada gaskiya ne.
Ya ce:
"Lallai Isa Ali yake nufi, mu dai ba mu san wani masallaci da ya gina ba, kuma don mutanensa sun yi raddi ai magana ta gaskiya ce."
Muhammad Rabiu ya ce babu wani batun kame-kame kowa ya san gaskiya duk abin da aka fada babu karya a ciki.
A cikin bidiyon, Sheikh Albaniy ya ce akwai wanda ya yi minista a Gombe amma bai tallafawa addini ba.
Abin da Albaniy ya ce kan Farfesa a Gombe
Sheikh Albaniy ya ce lokacin da yake minista bai gina masallaci ko da guda daya ba a matsayinsa na Musulmi.
Har ila yau, ya ce tsohon ministan bai tallafawa limamai ko ladanai ba a matsayinsu na wadanda ke hidima ga addini.
'Akwai wanda kuma ya yi hatta minista mai lasisi amma ba za ka daga masallaci kwaya daya da ya ginawa al'ummar jihar Gombe ba.

Kara karanta wannan
Sulhu da Turji ya bar baya da ƙura, an faɗi kuskuren da aka yi a tattaunawar a Zamfara
"Kuma ba za ka daga masallaci da ya taimakawa limamai ko ladanai ko wadanda suke hidimar addini wanda ya yi 'empoering' nasu ba.
"Malam Faruk Bamusa Allah ya ba shi lafiya zuwa ya yi ya gina katafaren kamfanin zazzabe shinkafa, mutum nawa suke cin amfanin wannan abin a jihar Gombe.?
"Bai samu mukamin komai ba bai da mukami lokacin ma da ya yi wannan abin bai nuna cewa yana neman wani mukami ba."

Source: Facebook
Masoyan Pantami a Gombe sun kare mai gidansu
Wannan bidiyo ya jawo martani inda wasu masoyan Isa Ali Pantami suka rika yada wani hoton masallaci cewa shi ya gina a Gombe.
Daga cikinsu akwai Abba Sani Pantami wanda ya ce Farfesa ya gina masallaci a cikin makarantar sakandare ta kimiyya da ke cikin birnin Gombe.
Abba ya wallafa hakan a Facebook inda ya ce Farfesa Pantami ya gina masallacin mai suna 'Masjidul Waalidayn' domin Allah wurin yin amfani da kudin aljihunsa ba na gwamnati ba.
Pantami ya taya Nafisa murnar lashe gasa
Kun ji cewa Sheikh Isa Pantami ya nemi a ba daliba, Nafisa Abdullah Aminu kyautar $100,000, gida da lambar OON bisa bajintarta a gasar TeenEagle.

Kara karanta wannan
'Babban bala'in da ke tunkaro mu': Shehi ya faɗi abin da Bello Turji ya faɗa masa
Nafisa ta doke ‘yan takara sama da 20,000 daga kasashe 69 a fagen harshen Turanci.
Pantami ya ce malaminta ma ya cancanci lada kamar yadda ake yi wa masu horar da ‘yan wasan kwallon Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng