Namadi: Kakkausar Gargadin Abba Kabir ga Mukarrabansa, Ya Ja Layi a Gwamnatinsa
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gargadi jami’an gwamnati su guji duk wani abu da zai bata sunan gwamnatinsa
- Ya bayyana hakan ne bayan murabus da kwamishinan sufuri Ibrahim Namadi Dala saboda alaka da wanda ake zargi da safarar kwayoyi
- Gwamnan ya ce gwamnati ba za ta lamunci taimakon masu laifi ba kuma duk mai hannu zai fuskanci hukunci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Bayan murabus din kwamishina a Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura gargadi ga mukarrabansa.
Gwamnan ya ce dole ne kowa ya zama mai gaskiya da rikon amana domin guje wa abubuwan da za su bata sunan gwamnati ko jefa matasa cikin hadari.

Asali: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Sanusi Bature D-Tofa ya bayyana a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Namadi ya yi murabus daga gwamnatin Abba
Hakan ya biyo bayan murabus din kwamishinan sufuri na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi Dala.
Ana zargin Namadi da alaka da masu safarar kwaya bayan ya yi belin shahararren mai sayar da kwaya, Sulaiman Danwawu.
Daga bisani, Abba Kabir ya kafa kwamitin bincike domin sanin dalilin belin dan kwayar bayan ce-ce-ku-ce daga al'umma.

Asali: Facebook
Abba ya fadi darasin dauka daga Namadi
Abba Kabir ya bayyana haka ne a yayin taron majalisar zartarwa karo na 30 da aka gudanar a gidan gwamnati Kano ranar Laraba, 6 ga watan Agusta, 2025.
Ya ce murabus da kwamishinan ya zama darasi ga sauran masu rike da madafun iko a jihar domin kauce wa aikata sabawa doka.
Sanarwar ta ce:
“Ba za mu yarda wani jami’i ya aikata laifi ko wani abu da zai kawo cikas kan abin da muka sanya a gaba ba, ko waye ne zai fuskanci hukunci."
Alkawuran Abba Kabir Yusuf ga 'yan Kano
Gwamna Abba ya ce duk wanda bai iya rike amana ba ya fi dacewa ya ajiye aiki tun kafin ya jawo wa gwamnati abin kunya.
Ya jaddada cewa yakin da gwamnati ke yi da safarar kwayoyi da miyagun dabi’u yana daga cikin ginshikan mulkinsa.
Ya ce duk wanda aka samu yana taimaka wa masu laifi kai tsaye ko a boye zai gamu da fushin doka ba tare da sassauci ba.
A ƙarshe, Gwamna Abba ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare gaskiya, adalci da bauta wa al’ummar Kano.
Bayana sun fito kan Ibrahim Namadi a Kano
Kun ji cewa rahoton Hukumar DSS ya sake bankado wasu bayanai game da Kwamishinan sufuri na Kano, Ibrahim Namadi game da belin dan kwaya.
An bayyana cewa Kwamishinan ya karɓi $30,000 daga Sulaiman Danwawu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi wanda ya jawo magana a jihar da Najeriya baki daya.
Gwamna Abba Yusuf ya fusata da wannan batu tare da kafa kwamiti, duk da cewa Namadi yana da dangantaka da Rabiu Kwankwaso wanda ake zargin ya hana daukar mataki mai tsauri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng