Sojoji Sun Kama Man Fetur da Kayan Tsafin da za a Mika wa Boko Haram

Sojoji Sun Kama Man Fetur da Kayan Tsafin da za a Mika wa Boko Haram

  • Dakarun Operation Hadin Kai tare da CJTF sun cafke wani da ake zargi zai kai wa Boko Haram man fetur a Maiduguri
  • Rahoto ya nuna cewa an kama wanda ake zargin ne a Muna da robobi a cikin buhu cike da man fetur da aka boye
  • A binciken farko, wanda ake zargin ya ce yana kan hanyarsa ta kai man zuwa Gamboru-Ngala a kan iyakar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno – Dakarun Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar CJTF sun kama wani da ake zargi da kai wa ‘yan ta’addan Boko Haram man fetur a birnin Maiduguri.

An kama wanda ake zargin, Ahmadu Mohammed Dogo, ne a Muna da misalin karfe 11:50 na safiyar Litinin, bisa sahihan bayanan sirri daga al’umma.

Kara karanta wannan

A karshe, Tinubu ya magantu game da 'yan Yobe da suka lashe gasar Turanci a London

Matashin da ake zargi da yi wa Boko Haram safarar kayayyaki
Matashin da ake zargi da yi wa Boko Haram safarar kayayyaki. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka kama mutumin a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken farko ya nuna cewa an tare shi ne yayin da yake yunkurin jigilar man fetur da aka saka a cikin kwalaben lemun “Fearless” da aka sanya a buhuna.

Dabarar mikawa Boko Haram fetur

Wanda ake zargin ya amsa cewa yana kan hanyarsa ce ta kai man zuwa garin Gamboru-Ngala da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Daily Post ta wallafa cewa sanarwar ta ce ana kyautata zaton Gamboru-Ngala wata hanya ce ta safarar kayayyaki ga ‘yan Boko Haram da ke yankin tafkin Chadi.

Matakin dakile hanyoyin kai kayan amfani ga ‘yan ta’adda na daya daga cikin muhimman manufofin rundunar tsaro a Arewa maso Gabas.

Dakarun tsaro sun bayyana cewa kama Dogo zai taimaka matuka wajen hana ci gaba da samun kayayyaki ga ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Bayan ikirarin mika wuya, yaran Turji sun yi kisa a mummunan harin da suka kai

Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: Defence Headquaters
Source: Facebook

An kama kayan maye da na tsafi

Baya ga kwalaben da ke cike da man fetur, an kuma gano wasu abubuwa da ake zargi kayan maye ne da kuma kayan tsafi.

Kayan da aka kwato sun hada da zobe, allurai, wasu miyagun kwayoyi da wasu abubuwa na sirri da ake kyautata zaton suna da nasaba da ta’addanci.

Jami'an tsaro sun ce an tsare wanda ake zargin a hannun sojoji inda ake ci gaba da masa tambayoyi.

An bukaci al’umma da su ci gaba da ba da sahihan bayanai don tabbatar da dorewar nasarorin da ake samu a yaki da ta’addanci.

Sojoji sun tsare wanda ake zargi

Ahmadu Mohammed Dogo dai na ci gaba da kasancewa a hannun jami’an tsaro, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike don gano sauran abokan aikinsa da ke taimaka wa ‘yan ta’adda.

Sojoji za su ci gaba da fantsama ko’ina domin tabbatar da cewa babu wata hanya da ‘yan ta’adda za su bi don samun kayan aiki.

Kara karanta wannan

"Mutuwa mai yankar ƙauna": Ango da abokinsa sun rasu kwana 2 bayan ɗaura aure

Yaran Turji sun kai hari Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga da ake zargi yaran Bello Turji ne sun kai hari Shinkafi a jihar Sokoto.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe wani mutum cikin matafiyan da 'yan ta'addan suka kai wa hari.

Hakan na zuwa ne yayin da aka fara samun labarin cewa Bello Turji ya ajiye makamai domin rungumar zaman lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng