'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Sha Azaba a Hannun Sojoji, an Tura Miyagu Barzahu

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Sha Azaba a Hannun Sojoji, an Tura Miyagu Barzahu

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu mayakan kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
  • Sojojin sun samu nasarar ne bayan sun yi wa 'yan ta'addan kwanton bauna a lokacin da suke tafiya cikin daji
  • Bayan sun fatattake su, jami'an tsaron sun kuma kwato makamai da kayayyaki daga hannun miyagun 'yan ta'addan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya da ke karkashin rundunar Operation Hadin Kai sun yi nasarar kashe wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne guda bakwai.

Dakarun sojojin sun hallaka 'yan ta'addan ne yayin wani kwanton bauna da suka shirya a kan hanyar Mayanti da ke yankin Dar El-Jamal, a jihar Borno.

Sojoji sun hallaka 'yan Boko Haram a Borno
Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun toshe kofofin tsira ga 'yan Boko Haram da ISWAP, an kashe miyagu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an Sojoji sun ragargaji Boko Haram

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Laraba, 6 ga watan Agustan 2025. Bayanan cewa harin kwanton baunar ya auku ne da yammacin ranar Talata.

Dakarun sun yi gaggawar kai harin ne a lokacin da mayakan suka fada tarko, inda aka kashe bakwai daga cikinsu.

An kuma gano wasu babura da sauran kayayyakin sufuri da kayan masarufi da ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.

Sojoji sun dakile harin 'yan Boko Haram

Sai dai, a cewar rahoton cikin bacin rai da fushin abin da ya faru, wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai farmaki a kauyen Dar El-Jamal da misalin karfe 7:30 na dare a ranar Talata din.

Sun shiga kauyen inda suka harbe-harbe ba kakkautawa don razana mazauna yankin.

Amma kafin su samu nasarar aiwatar da nufinsu, wata tawagar dakarun sojoji, ‘yan sa kai na CJTF da ƙungiyar maharba sun yi gaggawar kawo dauki.

Kara karanta wannan

Jami'an 'yan sanda sun kashe 'yan bindiga yayin arangama a Zamfara

Sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addan, kuma sun fatattake su zuwa daji cikin tsananin firgici.

Sojoji sun ragargaji 'yan Boko Haram a Borno
Sojoji sun kashe wasu 'yan ta'addan Boko Haram a Borno Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wannan lamari ya kara nuna yadda dakarun tsaro ke ci gaba da kara ƙaimi da himma wajen tabbatar da tsaro da hana ‘yan ta’adda sake samun kafa a yankunan da rikice-rikicen suka daɗe suna addaba.

Bincike da tabbatarwar da aka samu ya nuna cewa babu wani rauni ko asarar rai daga bangaren fararen hula ko jami’an tsaro yayin da aka dakile harin.

Wannan nasara na daga cikin jerin matakan da ake ɗauka don tabbatar da cewa an hana mayakan Boko Haram damar sake komawa da mamaye ƙananan yankunan da sojoji suka kwato.

Wasu sojoji sun hallaka 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan Boko Haram guda 17.

Sojojin sun hallaka 'yan ta'addan ne a wasu hare-hare da suka kai a jihohin Borno da Adamawa da ke yankin Arewa maso Gabas.

Jami'an tsaron sun kuma kwato makamai masu yawa tare da sauran wasu kayayyaki daga hannun 'yan ta'addan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng