Sarkin Kano, Sanusi II Ya Kawo Shawarar da Za Ta Ceto Ayyukan Mutane 10,000 a Kaduna

Sarkin Kano, Sanusi II Ya Kawo Shawarar da Za Ta Ceto Ayyukan Mutane 10,000 a Kaduna

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya shawarci gwamnatin tarayya ta gyara kamfanin auduga na Najeriya (UNTL) da ke Kaduna
  • Mai martaba ya bayyana cewa kamfanin na samar da ayyukan yi akalla 10,000, yana mai cewa rufe shi babbar matsala ce ga Arewa
  • Karamin ministan masana'antu, Sanata John Enoh ne ya jagoranci masu ruwa da tsaki ciki harda Sanusi II zuwa kamfanin a Kaduna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Sarkin Kano na 16, Dr. Muhammadu Sanusi II, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta farfado da masakar Najeriya (UNTL) da ke Kaduna.

Muhammadu Sanusi II ya ce gyara wannan kamfani zai ceto ayyukan mutane 10,000 daga salwanta a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
Sarkin Kano ya ba gwamnatin Tinubu shawarar ta gyara kamfanin yadi na Kaduna Hoto: @masarautarkano
Source: Twitter

Sarkin ya yi wannan roƙo ne a ranar Talata lokacin da ƙaramin ministan masana’antu, Sanata John Enoh, ya jagoranci rangadin haɗin gwiwa, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

A karshe, Tinubu ya magantu game da 'yan Yobe da suka lashe gasar Turanci a London

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta ziyarci masaka a Kaduna

A sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce ministan ya jagoranci wannan rangadi tare da masu ruwa da tsaki domin duba yadda za a farfado da ɓangaren masana’antar yadi, auduga da dinki a Kaduna.

Hakan na daga cikin matakan da Gwamnatin Tarayya ke ɗauka don farfado da masana’antu, karkashin manufa ta bakwai daga cikin ajendojin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

The Cable ta ruwaito cewa wannan ajenda ta kudiri aniyar samar wa ƴan Najeriya ayyukan yi, bunkasa masana'antu da farfaɗo da tattalin arziki.

Sarki Sanusi II ya ba Gwamnatin Tinubu shawara

Da yake jawabi a Kaduna, Sarki Sanusi ya ce:

“Rufe aikin wannan kamfani a 2022 abin damuwa ne, duba da tarihinsa na ɗaukar ma’aikata fiye da 10,000 a dukkan ɓangarorin masana’antar yadi, tun daga sarrafawa da saka, zuwa bugawa da dinki.
“Tasirin rugujewar UNTL a zamantakewa da tattalin arziki, musamman ga matasa da mata, na iya haifar da ƙaruwar rashin tsaro a yankin.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mummunar ambaliya a wurare 76 a Kano, Gombe da jihohi 17

“Saboda haka muna roƙon Gwamnatin Tarayya da ta magance matsalolin rashin wutar lantarki da ke dakatar da aikin kamfanin, shigo da yadi ta barauniyar hanya da ke rage darajar kayan gida da kuma kariyar haƙƙin mallaka, wanda ke hana sababbin ƙirƙire-ƙirƙire da zuba jari.”
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ya bayyana amfanin gyara kamfanin kera yadi na Kaduna Hoto: @Masarautarkano
Source: Twitter

Gwamnatin Tarayya ta fara ɗaukar matakai

A nasa jawabin, Sanata Enoh ya ƙarbi wannan ƙorafi tare da jaddada cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta ɗauki matakai da dama don farfado da wannan ɓangare.

Ya jaddada muhimmancin kamfanin UNTL a matsayin wani abu mai alaka da al’adu da tattalin arziki, inda ya ce sake farfadowar kamfanin zai dawo da ƙarfin gwiwa ga masana’antar yadi ta Najeriya.

Sanusi II ya ziyarci masoyinsa a asibiti

A wani rahoton, kun ji cewa Khalifa Muhammad Sanusi II , ya kai ziyarar jaje domin duba lafiyar wani matashi da ke cikin masoyansa mai suna Sadiq Gentle.

Sarkin ya kai ziyarar ne asibitin Murtala da ke cikin birnin Kano, inda aka kwantar da matashin bayan jin rauni a jikin sa sakamakon hari da aka kai masa.

Sanusi II ya bayyana cewa masarautarsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa an taimakawa matashin har ya samu lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262