Dan Majalisa Ya Tuna da Matattu, Ya Dauki Nauyin Gyaran Makabartu 80
- 'Dan majalisa wakilan Najeriya mai wakiltar Tsafe da Gusau ya dauki nauyin gyaran makabartu a mazabarsa
- Hon. Kabiru Maipalace ya kaddamar da aikin makabartun har guda 80 domin su kasance cikin yanayi mai kyau
- 'Dan majalisar ya bayyana cewa aikin gyaran makabartun yana da matukar muhimmanci domin yana kare bala'o'i
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Wani ɗan Majalisar Wakilai, Kabiru Maipalace, ya dauki nauyin gyaran makabartu 80 a ƙananan hukumomin Gusau da Tsafe na jihar Zamfara.
Kabiru Maipalace na wakiltar mazabar tarayya ta Gusau/Tsafe a majalisar wakilan Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ya kaddamar da ayyukan ne a garin Tsafe a ranar Talata, 5 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kaddamar da gyaran makabartu a Zamfara
A yayin kaddamar da aikin ɗan majalisar ya bayyana cewa wannan shiri wani ɓangare ne na ayyukan mazabarsa.
"A yau, mun kaddamar da gyaran makabartu 80 a ƙananan hukumomin Gusau da Tsafe a matsayin wani ɓangare na cikar shekaru biyu da na yi a zangon mulki na biyu a matsayin ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Gusau da Tsafe."
"Mun lura da yadda makabartu da dama suka lalace a sassa daban-daban na mazabata. Mu a matsayinmu na ’yan Adam, mun san cewa wata rana dukkanmu za mu tafi a binne mu a nan, don haka dole ne mu kyautata wannan wuri da zai zama makomar karshe gare mu."
"Kamar yadda muka sani a addinin Musulunci, akwai matuƙar muhimmanci a kula da tsaftar makabartu. Hakan yana hana aukuwar masifu da bala’o’i a cikin al’umma."
- Kabiru Maipalace
Kabiru Maipalace ya kuma yi alƙawarin biyan alawus ga masu gadin makabartu da ma’aikatansu, tare da samar musu da kayan aiki a kowane wata.
'Dan majalisar ya roki mutanen mazabarsa
Daga ƙarshe, ya roƙi al’ummar mazabarsa da su ƙara ƙaimi wajen yin addu’o’i don samun zaman lafiya da kawar da matsalar rashin tsaro a yankin, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar da wannan.
Ya roƙi al’ummar jihar da su ci gaba da goyon bayan manufofi da shirye-shiryen gwamnati domin inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A nasa jawabin, Hakimin Tsafe ta Gabas, Aliyu Abubakar, ya yaba wa ɗan majalisar bisa wannan ƙuduri, yana mai bayyana shi a matsayin ci gaba mai kyau da ya dace da bukatun al’umma.

Source: Facebook
Ya buƙaci sauran masu rike da mukaman siyasa da su yi koyi da ɗan majalisar ta hanyar kusantar al’ummominsu domin magance matsaloli da ƙalubalen da suke fuskanta.
"A madadin majalisar masarautar Tsafe, muna miƙa godiya ga ɗan majalisa da tawagarsa bisa ɗaukar nauyin ayyuka daban-daban domin rage matsaloli a cikin al’umma."
- Aliyu Abubakar
Gwamna ya nada sabon Sarkin Gusau
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya nada sabon sarkin Gusau.
Gwamna Dauda Lawal ya nada nadin Alhaji AbdulKadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau.
Nadin nasa da Gwamna Dauda ya yi, na da nufin maye gurbin mahaifinsa, marigayi Dr. Ibrahim Bello, wanda ya rasu bayan shafe shekaru 10 yana mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

