Gwamna Ya Kai Zuciya Nesa, Ya Tausayawa Jami'an Gwamnati 81 da Ya Dakatar
- Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya sassauta kan matakin da ya dauka na ladabtar da wasu daga cikin jami'an gwamnatinsa
- Francis Nwifuru ya dage dakatarwar da ya yi wa kwamishinoni 25 da wasu jami'an gwamnati kan kin halartar wani muhimmin taro
- Gwamnan ya umarce su da su dawo bakin aikinsu ba tare da bata wani lokaci ba domin dorawa daga inda suka tsaya wajen sauke nauyinsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya dage matakin dakatarwar da ya dauka kan jami’an gwamnatinsa guda 81.
Gwamna Francis Nwifuru dai ya hukunta jami'an gwamnatin ne saboda gazawa wajen halartar wani muhimmin taron gwamnati a jihar.

Source: Facebook
Wannan umarni na musamman na Gwamna Nwirufu ya fito ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Dr Monday Uzor, ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike kan zargin kwamishina da belin dilan ƙwaya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Nwifuru ya dakatar da kwamishinoni
An sanar da dakatarwar ne a ranar 28 ga Yulin 2025 wadda ta shafi babban lauyan gwamnati, kwamishinoni 25, manyan sakatarori 22, manyan mataimaka na musamman 14, da kuma mataimaka na musamman 24.
A cikin sanarwar da aka fitar, an ce an dakatar da jami’an ne saboda rashin halartar wani muhimmin taron gwamnati
An hana su sanya hannu kan takardun gwamnati tare da dakatar da biyansu albashi a lokacin dakatarwar.
Gwamna Francia Nwifuru ya yanke hukuncin cewa waɗanda abin ya shafa za su tafi hutun aiki na wata ɗaya ba tare da albashi ba.
An umurci kwamishinonin da su miƙa mulki da dukkanin kadarori ko takardun gwamnati da ke hannunsu zuwa ga manyan sakatarorin ma'aikatunsu.
Gwamnan Ebonyi ya dage dakatar da jami'an
Gwamnan ya kuma umurci dukkansu da su koma bakin aikinsu nan take ba tare da wani jinkiri ba, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Source: Facebook
"Mai girma gwamnan jihar Ebonyi, Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru, cikin jin kai, ya dage dakatarwar da aka yi wa jami’an gwamnati 81."
"Kwamishinoni da manyan mataimaka na musamman (SSAs), Mataimaka na musamman (SAs), da manyan sakatarori da abin ya shafa an umurce su da su koma bakin aikinsu nan take."
- Dr. Monday Uzor
Karanta karin wasu labaran kan gwamnan Ebonyi
- Gwamna Nwifuru ya ɗauki zafi, ya sallami hadimai 2 da aka gano sun yi rashin kunya
- Kwamishinoni 3 sun kai gwamna wuya a wurin taro, Nwifuru ya ɗauki mataki mai tsauri
- Gwamna Nwifuru ya fusata, ya umarci cafke kwamishinoni 5? An ji gaskiya
- Zargin rashawa: An ba gwamna wa'adin awa 48, ana so ya kori sakatariyar gwamnati
Gwamnan jihar Ebonyi ya kara albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Ebonyi, Francis Ogbonna Nwifuru ya kara albashi ga sababbin likitocin da aka dauka domin yin aiki a cibiyoyin lafiya matakin farko.

Kara karanta wannan
Dilan ƙwaya: Bayanai sun bulloƙo kan kwamishinan Kano, ana zargin ya karbi $30,000
Gwamna Nwifuru ya sanar da kara N500,000 a albashinsu domin samun damar gudanar da aikinsu cikin walwala.
Hakazalika ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe makudan kudade don siyo magunguna da gyara asibitocin da ake kwantar da marasa lafiya a fadin jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
