Sanusi II Ya Rufe Bakin Mutane, Ya Je Gidan Buhari domin Yin Ta'aziyya ga Iyalansa
- An tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a London, inda aka yi jana'izarsa a Daura ranar Talata 15 ga Yuli, 2025
- Ce-ce-ku-ce ya biyo bayan rashin ganin Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, a jana’izar, sai dai daga baya ya kai ziyarar ta’aziyya a Kaduna
- Mai Martaba Sanusi II ya bayyana cewa yana halartar taro ne a London lokacin da aka yi jana’izar marigayin, a yau ne ya je ya yi gaisuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - An tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar Lahadi 13 ga watan Yulin 2025.
Manyan yan siyasa da sarakunan gargajiya gargajiya sun samu halartar jana'izar marigayin a garin Daura da ke jihar Katsina.

Source: Facebook
Shafin Sanusi II Dyansty ya wallafa a Facebook cewa Sarkin Kano, Sanusi II ya ziyarci gidan marigayi Buhari a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jana'izar Buhari: An yi ta magana kan Sanusi II
Sarkin ya kai wannan ziyara ne bayan ce-ce-ku-ce da aka ta yi a bayan lokacin rasuwar marigayin a birnin London
Babban abin da ya fara jawo magana shi ne rashin ganin Sarki Sanusi II a wajen jana'izar Buhari da aka yi a ranar 15 ga watan Yulin 2025.
Wasu na cewa masoyan Mai martaba Aminu Ado Bayero ne ke maganganu saboda Sanusi II bai samu halarta ba.
Sai dai shi kuma Aminu Ado na gaba cikin waɗanda suka halarci jana'izar a ranar Talata 15 ga watan Yulin 2025.
An fadi dalilin rashin ganin Sanusi II a Daura
Daga bisani, makusancin Sanusi II da ake kira Muhammadu Dalhatu ya fitar da sanarwa kan dalilin rashin ganin basaraken yayin jana'izar.
Ya ce Sanusi II yana halartar wani taro ne a birnin London wanda shi ne dalilin rashin samun damar zuwa Daura.

Source: Twitter
Sanusi II ya ziyarci gidan Buhari a Kaduna
Sai dai a yanzu Sarkin ya ba marada kunya saboda tashi ya yi takanas ta Kano har gidan marigayin
Sarkin ya kai ziyarar ta'azziyar a yau Talata 5 ga watan Agustan 2025 domin jajantawa iyalan marigayin.
Yayin ziyarar, Sarkin ya yi musu jaje tare da addu'ar Ubangiji ya yi wa tsohon shugaban rahama da saka masa da gidan aljanna.
Sanarwar da aka fitar ta ce:
"Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, PhD, CON, ya kai ziyara gidan marigayi tsohon shugaban ƙasa, Janar Muhammadu Buhari, da ke Kaduna, domin yi wa iyalansa ta’aziyya.
"Sarki Sanusi II ya zai ziyarar a yau Talata, 5 ga watan Agustan shekarar 2025."
Sheikh Bello Yabo ya tabo batun yafewa Buhari
Mun ba ku labarin cewa Sheikh Bello Aliyu Yabo ya shawarci masu mulki su tuba kafin mutuwa, yana sukar wadanda ke neman a yafe wa Muhammadu Buhari.
Sheikh Yabo ya ce rashin mayar da dukiyar da aka wawure da kuma karancin nadama yana nuna cewa an yi zalunci da cin hanci ne da gangan.
Malamin ya koka da yadda 'yan Najeriya ke yafewa duk da halin kunci, yana cewa Allah ma yana da sharudda kafin yafewa mai zalunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


