Gwamna Buni Zai Karrama Daliban Yobe da Suka Doke Turawa a Gasar Duniya a London

Gwamna Buni Zai Karrama Daliban Yobe da Suka Doke Turawa a Gasar Duniya a London

  • Gwamnatin Yobe za ta shirya taron karramawa ga Nafisa Abdallah da Rukayya Muhammad bisa nasarar da suka samu a gasar duniya a London
  • Nafisa ta lashe gasar ƙwarewa a Turanci, yayin da Rukayya ta zama zakara a bangaren muhawara, dukansu ɗalibai ne a makarantar NTIC
  • Gwamna Mai Mala Buni ya yaba da nasarorin, yana mai cewa hakan na tabbatar da muhimmancin saka hannun gwamnati a harkar ilimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Yobe – Gwamnatin Jihar Yobe ta sanar da shirinta na karrama matashiya Nafisa Abdallah mai shekara 17 da kuma Rukayya Muhammad Fema mai shekara 15.

Za a karrama daliban ne bisa sakamakon nasarar da suka samu a gasar TeenEagle ta duniya da aka gudanar a birnin London, ƙasar Birtaniya.

Kara karanta wannan

'A bi a sannu,' Jagora a APC ya yi magana kan fara yi wa Tinubu kamfe

Daliban jihar Yobe da suka lashe gasar Turanci a London
Daliban jihar Yobe da suka lashe gasar Turanci a London. Hoto: Mamman Muhammad
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan jihar Yobe, Mamman Muhammad ne ya sanar da hakan a wani sako da ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin gasar da ta samu halartar 'yan takara sama da 20,000 daga ƙasashe 69, Nafisa ta zama zakarar gasar ƙwarewar harshen Turanci yayin da Rukayya ta lashe gasar muhawara.

Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana nasarorin a matsayin abin alfahari ga jihar da ƙasa baki ɗaya, yana mai cewa hakan na ƙara tabbatar da amfanin shirin tallafin karatu na gwamnatinsa.

Yobe ta yabawa wadanda suka lashe gasa

Gwamna Buni ya ce Nafisa da Rukayya sun nuna bajinta mai girma wanda ya tabbatar da cewa shirin tallafin karatu da gwamnati ke bayarwa na ƙara haɓaka ƙwarewar matasa.

Sanarwar ta ce:

"Dukkansu biyun, suna cikin ɗaliban da gwamnati ke daukar nauyin karatunsu gaba ɗaya a Makarantar NTIC,"

Ya ƙara da cewa nasarorin da suka samu sun fito ne daga jajircewa da ilimin da ake basu, wanda ke kara haskaka jihar da Najeriya a idon duniya.

Kara karanta wannan

A karshe, Tinubu ya magantu game da 'yan Yobe da suka lashe gasar Turanci a London

Yobe na cigaba da narka kudi harkar ilimi

Gwamna Buni ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da rage kuɗin makaranta da kuma ƙarfafa gina makarantun zamani ga kowane yaro a jihar.

Ya bayyana yadda gwamnatin jihar ta sake gina makarantu da dama da 'yan ta'adda suka lalata a baya, tare da samar da littattafai, kayan dakin gwaje-gwaje da kuma daukar malamai.

A cewarsa, kimanin ɗalibai 40,000 ne ke cin moriyar tallafin karatu daga gwamnatin jihar a manyan makarantu da jami’o’i a gida da waje.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni. Hoto: Mamman Muhammad
Asali: Facebook

Buni ya tunatar da wasu nasarorinsa a baya

Gwamnatin Yobe ta kuma bayyana yadda a kwanakin baya aka yi bikin yaye ɗalibai 167 da gwamnatin ta dauki nauyinsu zuwa ƙasashen waje, musamman a Indiya.

Rahotanni sun nuna cewa an yi bikin yaye dalibai ne da suka kammala karatu a fannonin kimiyya, kwamfuta da aikin likita.

Legit ta tattauna da Amina Bulama

Kara karanta wannan

Ana fargabar mummunar ambaliya a wurare 76 a Kano, Gombe da jihohi 17

Wata ma'aikaciya a jihar Yobe, Amina Muhammad Bulama ta yi wa Legit Hausa karin bayani kan makarantar da daliban suka halarta.

"Tabbas makarantar NTIC a Yobe ta ke, tsohon gwamnan mu, Mamman B Ali ne ya kawo makarantar saboda taimakon al'umma.
"Duk da cewa ana daukar mutane har yanzu, amma talakawa ba su cika samun gurbin karatu ba kamar da."

Pantami ya nemi a karrama dalibar Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Pantami ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta karrama dalibar jihar Yobe.

Daliba mai suna Nafisa Abdullahi ta lashe gasar Turanci da aka gudanar a birnin London na kasar Ingila.

Sheikh Pantami ya bayyana cewa ya kamata a karrama dalibar tare da malaminsu kamar yadda aka yi wa 'yan wasan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng