Sunan Tsohon Gwamna Ya Fito domin Maye Gurbin Sarki, Zai Zama Basarake na 44
- Majalisar masu nada Sarki na Olubadan ta zabi tsohon gwamna Rashidi Ladoja a matsayin wanda zai maye gurbin marigayi
- Masu nadin sarautar sun dauki matakin saka sunan Ladoja ne a Ibadan duk da cewa bai halarci taron da aka gudanar ba
- Oba Tajudeen Ajibola ne ya gabatar da sunansa, Oba Eddy Oyewole ya mara masa baya, za a aika sunan ga Gwamna Seyi Makinde
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - An fara daukar sunayen wadanda za su gaji kujerar Mai Martaba Sarki da ya rasu a Oyo da ke yankin Kudancin Najeriya.
Majalisar Olubadan ta zabi tsohon gwamnan jihar, Oba Rasidi Ladoja a matsayin Olubadan na 44 na Ibadan.

Source: Twitter
An zabi Oba Ladoja ne a wani taro da majalisar ta gudanar a sabon fadar Olubadan da ke Oke-Aremo, Ibadan, ranar Litinin, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Yobe: Bayan mutuwar Sarki, Gwamna Buni ya naɗa tsohon ɗan majalisar tarayya sarauta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutuwar Sarkin Ibadan ta rikita al'ummar Oyo
Wannan matakin na zuwa ne makwanni kadan bayan rasuwar Olubadan wanda ya shafe shekaru 90 a duniya.
Al'umma da dama sun shiga jimami a jihar Oyo biyo bayan rasuwar ɗaya daga cikin manyan sarakunan da ake tunƙaho da su.
Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya koma ga mahaliccinsa watanni bayan ya hau kan karagar mulki.
Marigayi Olakulehin ya yi bankwana da duniya ne kwanaki biyu bayan ya cika shekara 90 da haihuwa.

Source: Facebook
An saka sunan Ladoja domin zama Olubadan
Sai dai, Oba Ladoja bai halarci taron ba wanda dukan manyan sarakunan Ibadan masu rawani suka halarta, rahoton Punch ya tabbatar.
Balogun na Ibadan, Oba Tajudeen Ajibola, ne ya gabatar da kudurin, sannan Osi Olubadan, Oba Eddy Oyewole, ya mara masa baya.
Oba Ajibola, yayin jawabi a taron, ya ce za su mikawa Gwamna Seyi Makinde sunan Ladoja domin amincewa da nadin.
A gefe guda kuma, an zabi Ladoja ne bayan rasuwar Olubadan na 43, Oba Owolabi Olakulehin.
Lokacin da marigayin ya shafe a sarauta
Majiyoyi sun ruwaito cewa Oba Olakulehin ya karɓi sandar mulki ranar 12 ga Yuli, 2024, kuma ya rasu 7 ga Yuli, 2025.
Ya shafe kusan shekara ɗaya kacal a kan karagar mulki, yana da shekaru 90 a lokacin rasuwarsa wanda ya girgiza al'ummar Najeriya baki daya.
A cewar tsarin sarauta na Ibadan, an gano cewa Ladoja ne ke gaba a jerin masu jiran kujerar Olubadan wanda ya taba zama gwamnan Oyo.
Ladoja yana kan mafi girman mataki a tsarin hawa kujerar sarauta, kuma shi ne na gaba bayan Oba Owolabi.
Gwamna Buni ya nada sabon Sarkin Gudi a Yobe
A baya, mun ba ku ku labarin cewa Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da nadin tsohon ɗan majalisa a matsayin sabon Sarkin Gudi, bayan rasuwar marigayi Sarki.
Sabon Sarkin, Ismaila Ahmed Gadaka ya wakilci Fika/Fune a Majalisar Wakilai daga 2011 zuwa 2019 a majalisar tarayya.
Gwamna Buni ya bayyana kwarin gwiwarsa ga sabon Sarki, yana fatan zai kawo ci gaba da zaman lafiya a masarautar Gudi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
