Kwana Ya Ƙare: Baƙo Ya Gamu da Ajalinsa, Ya Rasu a Gidan Gwamnatin Jihar Neja
- Wani mutumi da ya kai ziyara gidan gwamnatin jihar Neja da ke Minna ya gamu da ajalinsa ranar 2 ga watan Agusta, 2025
- Rundunar ƴan sandan Neja ta ce baƙon mai suna, Gregory ya mutu ne kwatsam bayan ya yanke jiki ya faɗi a ɗaya daga cikin ɗakunan baki
- Tuni ƴan sanda suka kai gawarsa zuwa ɗakin ajiyar gawarwarki domin gudanar da bincike da nufin gano abin da ya yi ajalinsa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Minna, jihar Neja - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja ta tabbatar da mutuwar wani baƙo namiji bayan ya yanke jiki ya faɗi a gidan gwamnatin jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa mutumin ya kai ziyara ne gidan gwamnatin Neja da ke Minna, kuma bisa tsautsayi da ƙarar kwana, Allah ya yi masa cikawa a ɗaya daga cikin ɗakunan baƙi.

Kara karanta wannan
An tsinci gawar wata budurwa a kusa da Masallaci, ƴan sanda sun ga alamu 2 a wurin

Source: Twitter
The Cable ta gano cewa mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya bayyana sunan baƙon da ya rasu da Gregory.
Yadda baƙo ya rasu a gidan gwamnatin Neja
Ya ce mamacin ya ziyarci Sammy Adigun, shugaban kamfanin samar da abinci Niger Food Security Systems and Logistics Company Limited, lokacin da lamarin ya faru.
Rahotanni sun nuna cewa baƙon ya fara jin alamun rashin lafiya a tattare da shi jim kaɗan bayan da ya fahimci cewa wanda ya je nema ba ya nan.
An ce an yi gaggawar tuntubar ma'aikatan lafiya daga Asibitin Kwararru na IBB da ke Minna, amma tun kafin kai shi asibitin, mutumin ya riga mu gidan gaskiya.
Matakin da ƴan sanda suka ɗauka
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda ya fitar a ranar Litinin, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9:30 na dare, a ranar 2 ga Agusta, 2025, a cikin harabar gidan gwamnati.
“Ranar 2 ga watan Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 9:30 na dare, rundunar ‘yan sanda ta samu rahoton wata mutuwar ba zata daga jami’in tsaro na gidan gwamnati da ke Minna.
"Ya bayyana cewa wani baƙo da aka gano sunansa Gregory ya faɗi a galabaice, ko numfashi ba ya iya yi a ɗaya daga cikin ɗakunan baƙi na gidan gwamnati."
“Jami’an ‘yan sanda da ke caji ofis na GRA sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai shi Asibitin Kwararru na IBB da ke Minna, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa.”
- Wasi'u Abiodun.

Source: Twitter
Abiodun ya ƙara da cewa an ajiye gawar a dakin ajiye gawarwaki domin gudanar da binciken gano musabbabin mutuwar, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Gwamnatin Neja ta kori ma'aikatan shari'a 3
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Neja ta sallami wasu ma'aikata uku daga aiki cikinsu har da alƙalai daga aiki saboda aikata laifin karɓar rashawa.
Hukumar kula da harkokin shari'a ta Neja ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun sakatariyar hukumar, Hauwa Isah.
Daga cikin waɗanda aka kora akwai alkalin kotun Musulunci, Fatihu Hassan saboda ya karbi N800,000 daga shari'ar rikicin fili kuma ya jinkirta yanke hukunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
