Ranki Ya Dade: Yadda El Rufa'i Ya Zuba wa Matarsa Kalamai a Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarta

Ranki Ya Dade: Yadda El Rufa'i Ya Zuba wa Matarsa Kalamai a Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarta

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya ce zuba ruwan yabo ga matarsa Hajiya Asia da suka shafe kusan shekaru 26 tare
  • Tsohon gwamnan ya jinjina wa Asia, wacce ya bayyana a matsayin ginshiƙin da ya daidaita iyalinsu na tsawon kusan shekaru
  • El-Rufa’i ya yaba mata bisa yadda ta yi tsayin daka wajen tabbatar da kare hakkin bil adama da taimakon mara ƙarfi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya rubuta sakon godiya da yabo mai ratsa zuciya ga matarsa, Hajiya Asia Ahmad El-Rufa’i.

Wannan na zuwa ne yayin da take bikin zagayowar ranar haihuwarta, inda ya bayyana ta a matsayin “Hajiyarsa” abokiyar rayuwa da ginshikin da ke tallafa wa zaman lafiyar iyalinsu.

Kara karanta wannan

"Ina buƙatar ku sanya ni a addu'o'inku," Ministan Tinubu ya roƙi alfarmar ƴan Najeriya

Nasir El Rufa'i
Tsohon Kaduna na murnar zagayowar ranar haihuwar mai dakinsa Hoto: Nasir El–Rufa'i
Source: Facebook

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, El-Rufa’i ya bukaci ‘yan Najeriya da masoya su yaya shi da iyalinsa yi wa Asia addu’o’i.

El-Rufa’i yna zuba ruwan yabo ga matarsa

El-Rufa’i ya bayyana irin soyayyar da ke tsakaninsu yayin da take bikin zagayowar ranar haihuwarta a ranar 3 ga watan Agusta, 2025.

Bikin ya zo a daidai gaɓar da suke shirin cika shekara 26 da aure a ranar 14 ga watan Agusta, 2025.

Ya ce:

"Asia ta kasance abokiyar rayuwa da mai fahimta ga zuciyata fiye da kowacce mace – uwa ce ga ‘ya’yanmu gaba ɗaya kuma mai kula da su tsawon kusan shekara 30."
"Ta jure halaye na na musamman da rashin samuwata a gida saboda hidimar kasa, yayin da ita kuma ke bunƙasa basirarta da kuma bin abubuwan da take so.”

El-Rufa’i ya jinjina wa matarsa

El-Rufai ya yaba da irin kokarinta a fannin karatu, yana mai bayyana cewa tana da digiri na biyu har sau uku, kuma a yanzu haka tana kan karatun PhD.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: El Rufai ya debo ruwan dafa kansa, APC ta yiasa martani mai zafi

Tsohon gwamnan Kaduna
Tsohon gwamnan Kaduna ya yiwa mai dakinsa addu'a Hoto: Nasir El–Rufa'i
Source: Facebook

Baya ga nasarorin da ta samu a fannin karatu, El-Rufa’i ya bayyana irin rawar da Asia ke takawa a fannin kare haƙƙin ɗan adam, yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi,.

Haka kuma ya yabi yadda ta tashi tsaye wajen wayar da kai game da matsalolin kwakwalwa yayin da ƙware wa a matsayin lauya mai hidimta wa jama'a.

El-Rufa'i ya jawo wa kansa magana

A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar APC ta maida martani mai zafi ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, kan kalamansa da suka soki gwamnatin Bola Tinubu.

Jam’iyyar ta shawarci Malam El-Rufa’i da ya dakatar da yada manufofin siyasa ko kamfen din neman shugabanci, ya kuma jira har sai lokacin zaɓen 2027.

Sakataren APC na ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ne ya bayyana hakan bayan zafafan kalaman El-Rufa'i ga gwamnatin kan yadda ya ce ta gaza ta kowane fanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng