"Ba Zamu Iya Warware Matsalar Ƴan Najeriya ba," Ministan Tinubu Ya Fito Ya Tsage Gaskiya

"Ba Zamu Iya Warware Matsalar Ƴan Najeriya ba," Ministan Tinubu Ya Fito Ya Tsage Gaskiya

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya faɗa wa ƴan Najeriya gaskiya game da warware duka matsalolin da suke fuskanta
  • Nyesom Wike, tsohon gwamnan Ribas ya ce gwamnatin Bola Tinubu ba zata iya warware matsalolin Najeriya ba ko da za ta yi shekaru 20
  • Ya ce duk da haka gwamnati ta mayar da hankali wajen magance ƙalubalen da za su kawo sauƙin rayuwa kai tsaye ga jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (Abuja), Nyesom Wike, ya ce babu wata gwamnati da yake tsammanin za ta iya magance duka matsalolin Najeriya a wa'adi biyu.

Wike, taohon gwamnan Ribas, wanda ya yi shekara takwas ya ce ko da za a ba gwamnatin tarayya shekaru 20, ba ya tsammanin za ta iya magance matsalolin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

"Ina buƙatar ku sanya ni a addu'o'inku," Ministan Tinubu ya roƙi alfarmar ƴan Najeriya

Ministan Abuja, Nyesom Wike da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wike ya bayyana cewa gwamnati ba za ta iya warware duka matsalolin Najeriya ba Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Twitter

Ministan harkokin Abuja ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya yi bayani kan kokarin da gwamnatin Bila Tinubu ke yi na kawo ci gaba da kuma damuwar jama’a game da rashin kaddamar da wasu ayyuka da aka kammala a Abuja.

Gwamnatin Tinubu za ta iya gyara Najeriya?

A rahoton Tribune Nigeria, Wike ya ce:

"Ba zan yi maku ƙarya a nan ba, don haka ba kowace matsala muka warware ba zuwa yanzu, ba za a iya warware duka matsalolin kasar nan ba ko da wannan gwamnatin (Bola Tinubu) ta yi shekara 20 a mulki."

Mista Wike ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu tana ƙoƙarin warware matsalolin da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar mazauna birnin tarayya Abuja.

"A halin yanzu, gwamnati Tinubu tana ƙoƙarin warware matsaloli da za su taimaka wajen inganta rayuwar jama’a," in ji Wike.

Kara karanta wannan

"Shawarar da zan ba Atiku da ni ɗansa ne," Ministan Tinubu ya ɗauko tarihi tun daga 1999

Abin da ya hana kaddamar da ayyuka a Abuja

Dangane da dalilin da yasa ba a kaddamar da dukkan ayyukan da aka kammala a Abuja ba, ministan ya ce a yanzu gwamnati ta maida hankali ne kan wasu ayyuka.

“Ba zai yiwu mu kaddamar da kowane aiki ba. Muna daukar manyan ayyuka da suka lakume biliyoyin nlNaira don mu nuna wa jama’a.
"Amma idan ana batun kananan ayyuka, ba dole sai mun kaddamar da komai ba," in ji shi.
Wike tare da shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Ministan Abuja ya ce gwamnati na ƙoƙarin sauƙaƙa rayuwar ƴan Najeriya Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Wike ya nemi goyon bayan ƴan jarida

Wike ya bukaci kafafen yada labarai da su mara wa gwamnatin Tinubu baya ta hanyar ɗauko rahoton ayyukan da ke gudana, musamman a fannin ilimi da ci gaban al’umma.

“Ba za mu ce mun gama komai ba. Amma muna aiwatar da abubuwan da a kalla za su kawo sauyi a rayuwar mutane, wannan shi ne ainihin ma’anar shugabanci,” inji shi.

Wike ya roki addu'a daga ƴan Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Nyesom Wike, ya roƙi ‘yan Najeriya da su rika yi masa addu’a a kowace rana saboda ƙalubalen da yake fuskanta.

Kara karanta wannan

Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas

Ministan harkokin Abuja ya ce a yanzu ya maida hankali kan wasu jiga-jigai da suka ƙi biyan haraji a manyan unguwannin babban birnin ƙasar nan.

A cewarsa, duk da irin wahalar da yake fuskanta wajen tabbatar da doka kan waɗanda suke ganin sun fi karfin doka, yana buƙatar a sanya shi a addu'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262