An Kuma: Tinubu Ya Gwangwaje Ƴan Wasan D'Tigress da $100,000 da Gidaje a Abuja

An Kuma: Tinubu Ya Gwangwaje Ƴan Wasan D'Tigress da $100,000 da Gidaje a Abuja

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gwangwaje ƴan wasan ƙwallon kwandon Najeriya, da aka fi sani da D'Tigress
  • Shugaba Tinubu, wanda Sanata Kashim Shettima ya wakilta ya bai wa ƴan wasan D’Tigress lambar yabo ta kasa OON
  • Wannan ya biyo nasarar da suka samu gasar da aka buga ta ƙwallon kwandon a Abokan, inda suka lashe gasar karo na biyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara gwangwaje ƴan wasan Najeriya mata bayan sun yi nasara a gasar ƙwallon kwandon Afrika.

Tinubu ya bai wa duka ƴan wasan D’Tigress lambar yabo ta kasa bisa nasarar da suka samu a gasar Afrobasket ta mata ta 2025 da aka yi a ƙasar Ivory Coast.

Kara karanta wannan

Sabuwar ɓaraka ta danno cikin ADC ana tsaka da ƙoƙarin ganin bayan APC

Kungiyar ƙwallon kwando ta D'Tigress
Tinubu ya yiwa ƴan wasan D'Tigress kyautar $100,000 Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa baya ga haka, shugaban ƙasar ya kuma bai wa kowacce ƴar wasa kyautar $100,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan ya ware ƙarin $50,000 ga kowanne ɗan kwamitin ƙwallon kwando bisa nasarar da Najeriya ta samu.

Tinubu ya ba ƴan wasan D'Tigress kyauta

The Nation ta wallafa cewa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya wakilci Shugaba Tinubu wajen sanar da kyautar a bikin karɓar tawagar D’Tigress a ranar Litinin.

Haka kuma kowace ƴar wasa da jami’i a cikin tawagar za su samu gidan zama a babban birnin tarayya, Abuja.

A ranar Lahadi, tawagar Najeriya ta doke Mali da ci 78-64 a wasan ƙarshe da aka buga a filin Palais des Sports de Treichville da ke Abidjan.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
Tinubu ya yiwa D'Tigress kyautar gidaje Hoto: Bayo Onanuga
Source: Getty Images

Wannan nasarar ta sanya Najeriya ta kafa tarihi a matsayin ƙasar da ta fi kowane wata lashe kofin Afrobasket na mata sau biyar a jere.

Haka kuma, D’Tigress ta samu tikitin shiga gasar gasar cin kofin mata ta duniya ta shekarar 2026 da za a yi a Berlin, ƙasar Jamus inda za a fafata da su

Kara karanta wannan

Minista ya faɗi babban alƙawarin da Tinubu zai cika kafin ƙarshen wa'adinsa

Tinubu ya jinjina wa ƴan wasan Najeriya

A wajen bikin tarbar tawagar, Shugaba Tinubu ya karrama ƴan tawagar da lambar girmamawa ta OON bisa rawar da suka taka a wannan nasara da ta ba da damar cin kofin sai biyar.

Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci taron sun haɗa da Oluremi Tinubu, matar shugaban ƙasa da Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa.

Sai kuma Sanata Garba Maidoki, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin matasa da ci gaban wasanni da Kabiru Amadou, shugaban kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin wasanni.

Shugaban kasa ya karrama Super Falcons

A baya, kun ji Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya karrama ‘yan wasan Super Falcons bayan sun lashe gasar cin kofin mata ta Afrika.

A matsayin girmamawa bisa kwazon da suka nuna, Shugaba Tinubu ya bai wa kowacce ‘yar wasan ƙwallon ƙafan su 24 lambar girmamawa ta OON.

Shugaba Tinubu da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu, tare da wasu manyan jami’an gwamnati sun tarbi ‘yan wasan a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng