'Yan Bindiga Sun Tafka Barna yayin wani Mummunan Hari a Zamfara
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi aika-aika a jihar Zamfara bayan da suka kai wani harin ta'addanci
 - Miyagun 'yan bindigan sun kai harin ne a karamar hukumar Birnin Magaji inda suka yi awon gaba da wasu mutane tare da shanu
 - Majiyoyi na ganin cewa akwai yiwuwar 'yan bindigan sun kai harin ne saboda ayyukan wani dan sa-kai mai taimakawa jami'an tsaro
 
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun hari a kauyen Kasheshi Kura da ke cikin ƙaramar hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara.
Miyagun 'yan bindigan sun sace mutane biyar tare da sace shanu guda huɗu a safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 9:00 na safe.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
Rahotanni sun bayyana cewa harin na da alaka da wani ɗan sa-kai mai suna Ibrahim Shaibu, wanda aka fi sani da “Gwanda”, wanda memba ne na rundunar Askarawan Zamfara (CPG), wato masu kare al’umma.
Gwanda dai ya taɓa taimakawa jami’an kungiyar sa-kai ta Civilian Joint Task Force (CJTF), waɗanda aka fi sani da mafarauta lokacin da aka tura su wannan yanki.
Sai dai daga baya, waɗannan mafarautan sun janye daga yankin, wanda hakan ya bar Gwanda da sauran al’umma cikin haɗari.
Majiyoyi sun bayyana cewa akwai yiwuwar dangantakar Gwanda da jami’an tsaron na 'yan sa-kai ce ta sa ‘yan bindigar suka maida hankali wajen kai hari kan wannan kauye.
Wannan mummunan harin na 'yan bindiga ya jefa mazauna garin cikin fargaba da rashin tabbas dangane da tsaron rayuka da dukiyoyinsu.
Jami'an tsaro sun kai daukin gaggawa
Bayan aukuwar lamarin, jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike da kokarin ceto mutanen da aka sace tare da dawowa da shanun da aka sace.
Haka kuma, an ƙara tura jami’an tsaro zuwa wasu kauyukan dake makwabtaka da Kasheshi Kura domin hana kai hare-hare a nan gaba da kuma dakile barazanar ‘yan bindiga.

Source: Twitter
Al’umma na ci gaba da rokon gwamnati da ta ƙara kaimi wajen ƙarfafa tsaro da tura karin jami’an tsaro don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Wannan lamari yana ƙara bayyanar da irin matsalolin tsaro da jihar Zamfara ke fama da su musamman a yankunan karkara.
'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro na 'yan sanda sun samu nasara miyagun 'yan bindiga masu addabar mutane a Zamfara.
Jami'an 'yan sandan tare da hadin gwiwar 'yan sa-kai sun hallaka 'yan bindiga takwas bayan sun yi artabu da su a kauyen Fegin Kanawa da ke cikin karamar hukumar Gusau.
'Yan sandan sun yi arangama da 'yan bindigan ne lokacin da suka yi musu kwanton bauna a kan hanyar kai agajin gaggawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
    
