"Ina Buƙatar Ku Sanya Ni a Addu'o'inku," Ministan Tinubu Ya Roƙi Alfarmar Ƴan Najeriya
- Ministan harkokin Abuja, ya buƙaci ƴan Najeriya su sanya shi a addu'arsu ta yau da kullum saboda wahalar aikin da aka ɗora masa
- Nyesom Wike ya bayyana cewa yana fama da manyan mutane da shugabanni a ƙoƙarinsa na aiwatar da dokokin ƙasa a babban birnin tarayya Abuja
- Tsohon gwamnan ya ce mutane irinsa na buƙatar addu'a domin aikin da ke kansu yana da wahalar da ta wuce tunanin jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya roƙi ‘yan Najeriya da su rika yi masa addu’a a kowace rana saboda ƙalubalen da yake fuskanta.
Wike ya roƙi jama'ar Najeriya su sanya shi a addu'o'insu na yau da kullum saboda Allah ya taimake shi wajen aiwatar da dokoki a kan manyan mutane da ke ganin sun fi karfin doka.

Kara karanta wannan
"Shawarar da zan ba Atiku da ni ɗansa ne," Ministan Tinubu ya ɗauko tarihi tun daga 1999

Source: Facebook
Ministan ya bayyana haka ne a tattaunawar da ya saba yi da manema labarai a kowane wata a Abuja ranar Litinin, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane aiki ne a gaban Ministan Abuja?
Wike ya ce a yanzu ya maida hankali kan wasu jiga-jigai da suka ƙi biyan haraji a manyan unguwannin Abuja, yana mai ƙalubalantar yadda irin wadannan mutane ke ikirarin wakiltar talakawa.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su duba irin mutanen da ke zaune a manyan unguwannin birnin Abuja.
"Talakawa nawa ne ke zaune a Maitama da Wuse? Masu kudi ne suke ɗaukar hayar mutane su yi hira da ƴan jarida da sunan suna magana a madadin talakawa.
"Ku tambayi kanku, mutum nawa ne za su iya mallakar gida a Maitama? Talakawa nawa ke da kasuwanci a Maitama, Central Business Area, Wuse da Garki?” inji shi.
'Haraji yana da muhimmanci a kowace ƙasa'
Ministan ya kwatanta tsarin haraji na kasashen da suka ci gaba da na Najeriya, yana mai jaddada yadda kasar nan ke fama da matsin tattalin arziki.
“Duk wata gwamnati tana fama da matsalar ƙudin shiga, kuma wannan ne ya sa a kasashen da suka ci gaba ba sa wasa da batun haraji.
"A wasu wurare, kana iya tsira dada laifin kisan kai, amma ba za ka tsira ko ka kauce wa biyan haraji ba,” inji Wike.

Source: Facebook
Wike ya roki addu'a daga wurin ƴan Najeriya
Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya bayyana irin wahalar da ya ke sha wajen fuskantar waɗannan manyan mutane, rahoton Vanguard.
"Ya kamata ku rika mana addu’a kullum saboda irin abubuwan da muke gani da wahalhalun da muke fuskanta. Idan muka zaɓi yin abin da ya dace, sai a fara zaginmu," inji shi.
Ministan Abuja ya soki Atiku Abubakar
A baya, kun ji cewa Nyesom Wike ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, bisa yadda yake yawan sauya jam’iyya daga lokaci zuwa lokaci.
Ministan ya bayyana cewa tun bayan dawowar mulkin Najeriya dimokuradiyya a 1999, Atiku ya ke tsalle tsallen sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata.
Ya kara da cewa sauya shekar da ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa jam'iyyar haɗaka ta ADC a kwanan nan, ba wani sabon abu ba ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
