Obolo: Tsohon Minista Ya Gano Makircin da Aka Ƙulla a Shirin Ƙirƙiro Sabuwar Jiha a Najeriya
- Ƴan Najeriya aun shigar da buƙatun kirƙiro sababbin jihohi a tarukan sauraron ra'ayin jama'a kan gyaran kundin tsarin mulki
- Sai dai tun kafin kammala nazari kan buƙatun, an fara kokawa da zargin cewa wasu jihohin da ake son ƙirƙirowa suna tattare da gurɓatacciyar manufa
- Tsohon ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Cif Nduese Essien ya zargi masu fafutukar kirkiro jihar Obolo da shirya makircin ƙwace ƙasar Ibibio
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Yayin da Majalisar Tarayya ke ci gaba da aikin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, an fara hango ƙalubale a wasu bukatun da jama'a suka miƙa.
Ɗaya daga cikin buƙatun da aka fara ganin ba su dace ba akwai ƙirƙiro sabuwar jihar Obolo daga cikin jihar Akwa Ibom ta yanzu.

Source: Facebook
Tsohon minista ya yi fatali da ƙirƙiro jihar Obolo

Kara karanta wannan
"Ina buƙatar ku sanya ni a addu'o'inku," Ministan Tinubu ya roƙi alfarmar ƴan Najeriya
A rahoton da Leadership ta wallafa, tsohon minista a Najeriya, Cif Nduese Essien, ya ce waɗanda suka nemi a ƙirkiro jihar Obolo suna da wata manufa mara kyau a zuƙatansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Essien, Tsohon Ministan Ƙasa, Gidaje da Raya Birane, ya yi gargaɗi kan abin da ya kira shirin boye na kwace albarkatun Ibibio land da sunan kirkiro sabuwar jiha.
Mecece manufar masu son raba jihar Akwa Ibom?
Ya ce ‘yan kabilar Obolo da ke gabashin Obolo, Oron a Akwa Ibom, da kuma Opobo (Andoni) daga makwabciyar Jihar Ribas sun jima suna fafutukar ƙwace ƙasar Ibibio.
A cewarsa, wannan fafutuka da suka ɗauki shekaru masu yawa suna yi ba za ta yiwu ta hanyar doka ko siyasa ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Essien, wanda ya taɓa rike kujerar Majalisar Wakilai, ya tuna tarihin yadda ake ƙokarin mamaye gabar ruwan Ibibio tun shekaru 100 da suka wuce.
Cif Nduese Essien ya samu goyon bayan jama'a
Da yake zantawa da manema labarai a taron ƙungiyar al’adu mafi girma ta Mboho Mkparawa Ibibio (MMI), tsohon ministan ya ce:
“A yau, waɗannann mutanen sun haɗa kai da wasu mutane daga jihohin maƙwabta sun sake ɓullo da shirin ƙwace Ibibio land da sunan kirkiro sabuwar jihar Obolo.

Kara karanta wannan
"Ba mu buƙatar kuɗi," Kasurgumin ɗan bindiga, Sani Black ya zo da sabon salo a Zamfara
"Ina mai tabbatar maku da cewa za mu daƙile duk wani yunkuri na karɓe mana Ibibio land. Mun gano makircin da suke ƙullawa kuma ba za mu bari a ƙwace kowane yanki a kasar Ibibo ba.

Source: Facebook
Jawabin Cif Essien ya samu gagarumar karɓuwa da tafi daga mahalarta taron, wadanda suka haɗa da sarakunan gargajiya, manyan jami’an gwamnati, ƙwararru, shugabannin matasa da ‘yan jarida.
An nemi ƙarin jihohi 8 a Arewa maso Yamma
A wani labarin, kun ji cewa masu ruwa da tsaki a Arewa maso Yammacin Najeriya sun buƙaci ƙarin jihohi takwas daga cikin bakwai da ake da su a yankin.
Sun miƙa wannan buƙata ne a wurin taron da Majalisar Dattawa ta shirya don sauraron ra'ayoyin jama'a kan gyaran kundin tsarin mulki a jihar Kano.
Shugabanni, sarakuna, ƴan jarida da fararen hula sun halarci taron na kwanaki biyu don gabatar da ra’ayoyinsu domin la’akari da su a gyaran kundin mulkin da Majalisar Tarayya ke yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng