Sarautar Kano: Sarkin Kofa Ya Dawo Bangaren Sanusi II, Ya Yi Watsi da Aminu Ado

Sarautar Kano: Sarkin Kofa Ya Dawo Bangaren Sanusi II, Ya Yi Watsi da Aminu Ado

  • Balarabe Sarkin Kofa ya tuba a gaban Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammad Sanusi II saboda rashin biyayya da ya nuna a baya
  • Rahotanni sun nuna cewa a gaban manyan 'yan fada ya furta kalmomin tuba tare da yin mubaya’a ga Mai Martaba Sarkin
  • Ya janye goyon bayansa ga fadar Nasarawa, ya kuma bukaci afuwa bisa goyon bayan da ya baiwa Aminu Ado Bayero a baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Balarabe Kofa wanda aka fi sani da Sarkin Kofa ya bayyana yana tuba a fadar mai martaba Khalifa Muhammad Sanusi II.

Balarabe Sarkin Kofa ya nemi gafara da kuma tuba bisa rashin biyayya da ya yi wa Sanusi II a baya.

Sarkin kofa ya fita daga bangaren Aminu Ado, ya koma wajen Sanusi II
Sarkin kofa ya fita daga bangaren Aminu Ado, ya koma wajen Sanusi II. Hoto: Masarautar Kano
Source: Twitter

Legit Hausa ta gano cewa a yau Litinin, 4 ga Agusta, 2025 Masarautar Kano ta wallafa labarin a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Bayan bidiyon Ummi Nuhu, Mai Dawayya ya yi tone tone, ya faɗi shura da ya yi a baya

Wannan na zuwa ne yayin da rikicin sarauta a Kano ke ci gaba, inda Sarki Aminu Ado Bayero ke ta zama a fadar Nasarawa duk da sauke shi da gwamnatin Kano ta yi.

Sarkin Kofa ya yi mubaya’a ga Sanusi II

A cikin jawabin nasa, Sarkin Kofa ya bayyana cewa ya gane gaskiya ne bayan dogon tunani, kuma ya yanke shawarar dawowa daga goyon bayan da ya bai wa bangaren Nasarawa.

A yayin da yake gaban mai martaba tare da wasu 'yan fada, Sarkin Kofa ya furta cewa:

"Tuba nake ranka ya dade,"

A daya bangaren kuma, sauran 'yan majalisa na amsawa da cewa:

"Tuba yake ranka ya dade."

Ya roki Mai martaba sarkin da ya gafarta masa bisa duk wani kuskure da ya aikata, yana mai cewa yanzu ya gano gaskiya.

Ya kuma yi mubaya’a a fili ga Khalifa Muhammad Sanusi II a matsayin wanda ya yarda da cewa shi ne halastaccen Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Bayan barin kujerar APC, Hadimin Ganduje ya zargi Gwamnatin Tinubu da son kai

Mai martaba Muhammadu Sanusi II a fadar shi
Mai martaba Muhammadu Sanusi II a fadar shi. Hoto: Masarautar Kano
Source: Facebook

Asalin matsayin Sarkin Kofa a fada

Sarkin Kofa na daya daga cikin manyan mukamai da suka dade suna da tarihi a cikin tsarin masarautun Arewa.

A da, kowace kofa ta birnin Kano tana da wanda ke da alhakin sa ido da tsaro a cikinta, wanda shi ne Sarkin Kofa.

Ayyukansa sun hada da kiyaye shiga da fita na birni, da rubuta bayanan baki da 'yan ƙasa masu wucewa.

A lokacin yaki, umarni daga Sarki ko daga Sarkin Yaki ne kawai ke aiki, amma a lokacin zaman lafiya, Sarkin Kofa ke da cikakken iko da kofa.

Rikicin sarautar Kano ya ki karewa

Rikicin sarautar Kano ya samo asali ne tun bayan sauke Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsige, tare da dawo da Sanusi II.

Tun daga lokacin, bangaren Aminu Ado ya dauki matakin shari’a don kalubalantar sauke shi da aka yi.

Kara karanta wannan

Kano: Minista ya faɗi wanda suke son ba takara a APC domin ƙwace kujerar Abba

Duk da rikicin har yanzu yana kotu, wannan mataki na Sarkin Kofa na iya zama wata alama ta sauyin ra’ayi daga wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a masarautar.

Kwankwaso ya hadu da Aminu Ado a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran NNPP a Najeriya ya hadu da mai martaba Aminu Ado Bayero a Abuja.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya hadu da Sarkin Kano na 15 ne a wajen wani taron kaddamar da littafi a birnin tarayya.

Taron ya samu halartar fitattun 'yan siyasar kasar nan, ciki har da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng