Ojulari: Shugaban NNPCL Ya Kawo Karshen Jita Jita kan Batun Murabus Dinsa
- An yi ta yada jita-jita kan cewa shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari ya yi murabus daga kan mukaminsa
- Jita-jitar da aka yada, ta sanya har EFCC da DSS sun fito sun musanta tilastawa Ojulari yin murabus baya an yi zargin cewa akwai hannunsu a ciki
- Sai dai, a ranar Litinin, 4 ga watan Agustan 2025, shugaban na kamfanin NNPCL ya shiga ofis domin ci gaba da gudanar da ayyukansa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bashir Bayo Ojulari, ya koma bakin aikinsa.
Bashir Bayo Ojulari ya iso ofis dinsa kusan ƙarfe 9:35 na safiyar Litinin, 4 ga watan Agustan 2025.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce wani babban jami’in tsaro ya tabbatar mata da batun komawar shugaban na kamfanin NNPCL bakin aikinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayo Ojulari ya dawo bakin aiki a NNPCL
Jami'in ya bayyana cewa Bayo Ojulari yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na yau da kullum kamar yadda aka saba.
Ma'aikacin ya bayyana cewa an aika da wata sanarwa ta cikin gida ga ma’aikatan NNPCL da su yi watsi da labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Ojulari ya yi murabus.
"Da kimanin karfe 9:35 na safe, Bayo Ojulari, shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), ya iso ofishinsa. A halin yanzu yana ci gaba da gudanar da ayyukansa na yau da kullum.
"Har ila yau, an aika da takardar tunatarwa ta cikin gida ga ma’aikata da su yi watsi da labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta game da jita-jitar murabus ɗinsa."
- Wata majiya
A karshen makon da ya gabata ne rahotanni da dama suka bayyana cewa Ojulari ya yi murabus, amma babu wata sanarwa a hukumance har zuwa yau da ya koma ofishinsa.
Shugaban kamfanin NNPCL ya halarci taro
Hakazalika, an ga shugaban na kamfanin NNPCL a wani taron da ƙungiyar injiniyoyin man fetur ta kasa ta shirya a Legas a ranar Litinin.
Wani bidiyo da mahalarta taron suka rabawa Daily Trust ya nuna Ojulari, wanda shi ne ɗaya daga cikin manyan masu jawabi, yana isar da saƙonsa ta hanyar amfani da manhajar Zoom.

Asali: Twitter
A baya-bayan nan an samu jita-jita dangane da cewa fadar shugaban ƙasa ta sauke Ojulari daga mukaminsa a cikin wani yanayi masu cike da ce-ce-ku-ce.
Duk da cewa babu wata sanarwa ta hukuma daga fadar shugaban ƙasa ko kamfanin NNPCL, bayanan da aka fitar a ranar Laraba sun nuna cewa aiki na ƙarshe da Ojulari ya gudanar a hukumance shi ne taron tattaunawa da ma’aikatan kamfanin da aka yi a hedkwatar NNPCL da ke Abuja.
EFCC ta musanta kama shugaban NNPCL
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta musanta batun cewa ta dauke shugaban kamfanin NNPCL, Bayo Ojulari.
EFCC ta bayyana cewa ko kadan babu hannun shugabanta kan zargin cewa ya tilastawa shugaban na NNPCL yin murabus.
Sai dai ta bayyana cewa ta samu korafi daga wajen wasu mutane masu neman a gudanar da bincike a kansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng