'Yan Sanda Sun Harbe 'Dan Limamin Abuja, Ya Mutu har Hahira
- An zargi ‘yan sanda da harbin ɗan limamin Kuchibuyi, Attahiru Abubakar, har lahira a rikicin filin da ya barke a yankin Bwari
- Rahoto ya nuna cewa wani ɗan uwan mamacin ma ya jikkata sakamakon harbin bindiga da aka masa yayin rikicin da aka yi a Abuja
- ‘Yan sanda sun je wajen ne domin kawo zaman lafiya, amma mazauna yankin na zargin su da harbin jama’a da kama samari da dama
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rikicin fili a Kuchibuyi da ke ƙarƙashin yankin Bwari a birnin tarayya Abuja ya rikide zuwa bala’i bayan da wani ɗan limamin garin, Attahiru Abubakar, ya rasa ransa.
Rahotanni sun bayyana cewa dan limamin ya rasu ne sakamakon harbin bindiga da ake zargin ‘yan sanda ne suka yi masa.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa lamarin da ya faru a ranar Asabar ya haifar da fargaba a yankin, inda wani ɗan uwan mamacin, Abass, ya jikkata sosai kuma yana jinya a asibiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An harbe dan limami a Abuja
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga ƙoƙarin wani mutum da ya yi yunkurin karɓe filin jama’a ba tare da amincewar su ba.
Wani ɗan uwan mamacin, Sanusi Abubakar, ya bayyana cewa:
“Bayan da wasu matasa suka hana motoci wucewa, lamarin ya lafa. Amma daga baya, ‘yan sanda suka dawo suka fara harbe-harbe.”
Legit ta rahoto ya ƙara da cewa:
“Dan’uwana Attahiru ya mutu nan take, Abass kuma yana asibiti. Har mahaifinmu limamin garin an harbe shi.”
Bayanin da 'yan sandan Abuja suka yi
Rundunar ‘yan sandan Abuja ta ce sun samu kiran gaggawa ne game da rikicin da ya biyo bayan takaddama kan fili, kuma suka aika jami’ai daga sassan Byazin da Kubwa.

Kara karanta wannan
Mutanen gari da 'yan sanda sun yi arangama da 'yan sanda a Abuja, an samu asarar rai
Mai magana da yawun rundunar, Josephine Adeh, ta ce:
“Bai kamata matasa su kai hari ga jami’an tsaro da ke bakin aiki ba. Doka za ta yi aiki kan duk wanda ya aikata hakan.”
Sai dai al’ummar yankin sun soki bayanin ‘yan sanda, inda suka ce bai bayyana gaskiyar abin da ya faru ba.
Sun yi suka suna masu cewa ba a fadi cewa mutane uku sun jikkata sakamakon harbin bindigar da aka yi ba.

Source: Facebook
Wani mazaunin yankin da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce:
“A gaskiya ‘yan sanda sun harbi mutane. Attahiru ya mutu nan take. Sannan sun kama wasu samari guda shida.”
Ya ƙara da cewa mutumin da ke son kwace filin ya zo da sojoji tun kafin wannan rana, sannan daga baya ya kawo ‘yan sanda suka fara harbe-harbe.
Hotunan da suka bayyana sun nuna gawar Attahiru da harbin bindiga a ƙirji, lamarin da ya ƙara jefa jama’a cikin firgici da kuka.
Soja ya mutu a hadarin mota a Yobe

Kara karanta wannan
"Ba mu buƙatar kuɗi," Kasurgumin ɗan bindiga, Sani Black ya zo da sabon salo a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa tawagar sojojin Najeriya ta hadu da tsauyayi a hanyar Damaturu/Jos a jihar Yobe.
Bayanan da Legit Hausa ta tattataro sun nuna cewa wani jami'in soja daya da ya samu munanan raunuka ya rasa rai nan take.
Bayan hadarin, jama'ar da ke kusa da wajen sun kai agaji kuma an tafi da sojojin da suka yi rauni zuwa asibiti domin ba su kulawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
