Sun Aikata Manyan Laifuffuka: Gwamnati Ta Kori Manyan Alkalai 2 daga Aiki a Neja

Sun Aikata Manyan Laifuffuka: Gwamnati Ta Kori Manyan Alkalai 2 daga Aiki a Neja

  • Hukumar kula da shari'a ta Neja ta kori manyan jami'ai uku ciki har da alkalai biyu, bisa karbar rashawa da rashin gaskiya a aiki
  • JSC ta sallami Chief Magistrate Isaac Yisa da magatakarda Muhammad Ahmed saboda karbar rashawa da bayar da beli ba bisa ka’ida
  • An kori alkalin kotun Musulunci, Fatihu Hassan saboda ya karbi N800,000 daga shari'ar rikicin fili kuma ya jinkirta yanke hukunci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Hukumar kula da ayyukan shari’a ta jihar Neja ta kori alkalan kotu biyu da babban magatakarda bisa zargin aikata manyan laifuffuka masu alaka da cin amanar aiki da rashin da’a.

A cewar wata sanarwa daga sakataren hukumar, Hauwa Isah, an dauki wannan mataki ne domin kare mutunci da amintaccen tsarin aikin shari’a a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Katsina ta waiwayi manyan asibitocin jihar

Hukumar JSC ta jihar Neja ta kori wasu alkalai biyu da magatakarda daya daga aiki
Hukumar JSC ta jihar Neja ta kori wasu alkalai biyu da magatakarda daya daga aiki. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

An kori alkali da magatakardar kotu

Sanarwar, wacce gidan talabijin na AIT ya rawaito, ta ce an yanke wannan hukunci ne bayan cikakken nazari da tattaunawa da mambobin hukumar suka yi bisa rahoton kwamitocin bincike da aka kafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitocin dai an kafa su ne domin bincikar korafe-korafen da aka shigar kan wadannan ma’aikatan bisa zargin aikata wasu laifuffuka da cin zarafin ofis.

Daga cikin hukuncin da aka yanke, hukumar ta kori Chief Magistrate Isaac Yisa na kotun majistare ta Kontagora da kuma magatakardar kotun, Muhammad Ahmed, daga aiki nan take.

Bisa rahoton da aka gabatar, an gano cewa laifuffukan da suka aikata sun hada da karbar rashawa daga hannun mai kara domin ba da beli.

Sauran laifuffukan sun hada da hana beli ko bayar da beli ba tare da bin ka’ida ba, da kuma rashin rubuta bayanan shari’a yadda ya kamata.

Neja: An kori alkalin kotun musulunci

Kara karanta wannan

'Za a rataye shi': Kotu ta yanke wa malamin Musulunci hukuncin kisa a jihar Kwara

An kuma gano cewa rajistan kotun, Muhammad Ahmed, ya karbi N10,000 a cikin asusun bankinsa a matsayin rashawa kafin ya cika takardar beli da sammacin sakin mai kara da aka tsare.

Haka kuma, hukumar ta kori alkalin babbar kotun shari’ar Musulunci da ke Wushishi, Fatihu Hassan, saboda karbar N800,000 daga wani mai kara a wata shari’ar rikicin fili da ke gabansa, sannan kuma ya ki yanke hukunci kan shari’ar.

Sanarwar ta ce wadannan ayyuka da ma’aikatan suka aikata sun sabawa wasu sassa na dokokin hukumar kula da ayyukan shari’a ta jihar Neja na shekarar 2018, wanda ya sa aka kori ma’aikatan karkashin sashi na 61 na dokokin.

Hukumar shari'a ta jihar Neja ta sha alwashin ladabtar da duk wani ma'aikacin shari'a da aka kama da rashawa ko cin amanar ofis
An sallami alkalai 2 daga aiki a Neja bayan an kama su suna karbar rashawa da karya dokokin aiki. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

JSC ta tilasta magatakarda yin ritaya

Baya ga hakan, Hukumar ta tilasta wa Ramatu Suleiman, magatakardar kotun shari’a ta Bida, yin ritaya daga aiki saboda samun rikici da rashin daidaito a gudanar da wasu ayyuka.

An gano cewa Ramatu tana aiki da wani kamfani a matsayin kwamishinar RIFAN duk da cewa tana cikin ayyukan ma’aikatar shari’a ta Neja.

Rahoton ya ce abin da Ramatu ta yi ya sabawa sashe na 58(1)V na dokar hukumar da kuma hukuncin kora karkashin sashe na 61.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya fara gwangwaje jihohin Arewa da titunan jiragen kasa

An kori ma'aikatan shari'a a Jigawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar shari’a ta jihar Jigawa ta kori ma’aikanta uku saboda cin amanar aiki da karya dokokin tsarin aikin shari’a.

An bai wa wasu alkalan kotunan shari’a uku shawarar yin murabus saboda sakacin aiki da aikata kuskuren shari’a sau da dama.

Hukumar JSC ta jihar Jigawa ta nanata aniyarta na tabbatar da tsabtar tsarin shari’a tare da ladabtar da duk masu aikata rashin gaskiya a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com