Wata Sabuwa: Likitoci a Asibitin Koyarwa Sun Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

Wata Sabuwa: Likitoci a Asibitin Koyarwa Sun Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani

  • Likitocin asibitin LAUTECH sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda gazawar gwamnati na biya masu bukatunsu
  • A wasikar da suka aikawa shugabannin asibitin, likitocin sun ce sun ba da wa’adin mako uku kafin su ɗauki matakin yajin aikin
  • Bukatunsu sun haɗa da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi, biyan kudin kayan aiki, gyaran ɗakuna da dai sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo – Likitoci karkashin kungiyar ARD a asibitin koyarwa na LAUTECH, da ke Ogbomoso, jihar Oyo, ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani.

Likitocin sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon gazawar shugabancin asibitin da kuma gwamnatin jihar wajen magance korafe-korafen da suka dade suna yi.

Likitoci sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani kan gazawar gwamnati na cika alkawuranta
Kofar shiga asibitin LAUTECH da ke Ogbomoso, jihar Oyo, inda likitoci suka shiga yajin aiki. Hoto: @MedicalworldNig
Source: Twitter

Yajin aikin farko da likitocin suka shiga

A baya, a ranar 8 ga Afrilu, 2025, likitocin sun dakatar da wani yajin aikin wata guda, don ba gwamnati da asibiti dama su cika bukatun da aka gabatar, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Ba mu janye ba,' malaman jinya sun 'kunyata' ministan lafiya kan batun yajin aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai bayan wucewar watanni uku, sun sake aika takarda zuwa ga shugaban asibitin LAUTECH, Farfesa Olawale Olakulehin, inda suka bayar da wa’adin makonni uku don a cika ragowar bukatunsu.

Wasikar mai kwanan wata 8 ga Yuli mai taken “sanarwar yajin aiki”, ta ce za su tura wasiku ga dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnatin jihar da asibitin.

A cikin wasikar, suka ce:

“Majalisar kungiyar ARD-LAUTECH ta amince da bayar da wa'adin makonni uku, wanda a wannan lokacin ne za mu sanar da hukumomi shirin mu na yajin aiki.
“Mun yaba da kokarin shugabancin jami'ar wajen biyan wasu daga cikin bukatunmu, musamman kudin karin matsayi da dawo da kudin jarrabawa.”

Bukatun da likitocin suke so a biya masu

Sai dai, sun bayyana takaicinsu cewa duk da wannan ci gaba, an gaza biya masu wasu mahimman bukatu har zuwa yanzu.

Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan

ASUU, SSANU: Ma'aikatan jami'a sun fusata, sun shiga yajin aikin sai baba ta gani

“Bukatun da ba a cika ba sun haɗa da aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi da biyan bashin albashin da ya fara daga Janairun 2025, kudin kayan aiki, da gyaran ɗakunan kwana.”

Sun kuma ambaci cewa suna bukatar a fitar da kudin asusun tallafawa likitocin ARD da kuma daukar sababbin likitoci masu neman kwarewa a dukkan sassan asibitin.

“Matsalolin da muke fuskanta suna bukatar kulawar gaggawa. Mun gaji da jira – yanzu lokaci ne na daukar mataki,” a cewar sanarwar.
Likitocin asibitin koyarwa na LAUTECH sun ce ba za su koma aiki ba sai an biya bukatunsu
Wasu likitoci na kan gudanar da tiyata a wani asibiti. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Likitoci sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani

A cikin sanarwar, ƙungiyar ta bayyana cewa idan gwamnati da shugabannin asibitin suka kasa cika bukatun nan zuwa 29 ga Yulin, 2025, za su fara yajin aiki na baba-sai-ta-gani.

Ganin ba a biya bukatun ba, ya sa likitocin, a ranar 28 ga Yulin 2025, suka sake turawa shugabannin asibitin da gwamnati sabuwar wasika, wacce ta ce:

“Saboda gazawar gwamnati da shugabannin asibitin na cika alkawuran da suka dauka, za mu fara yajin aiki daga ranar Litinin, 29 ga Yulin, 2025.”

Likitocin sun ce jan kafar da aka samu daga gwamnati ko asibitin ne ya tilasta su daukar wannan mataki, kuma suna fatan za a gaggauta biya masu bukatunsu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan farmaki kan manoma a Sokoto, an samu asarar rayuka

Malaman jinya sun shiga yajin aiki

A wani labarin, mun ruwaito cewa, malaman asibiti 25,000 a karkashin NANNM sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki bakwa.

Yajin aikin zai shafi dukkanin asibitocin gwamnatin tarayya 74, da na jihohi 36, FCT da kananan hukumomi 774 a fadin kasar nan.

NANNM na bukatar aiwatar da tsarin albashi, karin kayan aiki, daukar ma’aikata, da kuma dakatar da rage kudin alawus ga malaman jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com