Kungiyar ARD ta shiga yajin aikin kwanaki 3 a asibitin Jami’ar Ogun a Yau

Kungiyar ARD ta shiga yajin aikin kwanaki 3 a asibitin Jami’ar Ogun a Yau

- Kungiyar ARD ta likitoci na reshen Jami’ar OOUTH a Ogun za su fara yajin aiki

- Likitocin sun ce za su fara yajin aiki a yau ne saboda an ki biya masu bukatunsu

- Daya daga cikin kukan Likitocin shi ne an ki fara biyan karin albashin da aka yi

Kungiyar ARD ta likitocin da ke karatun zama kwararru a Najeriya na reshen asibitin koyon aiki na jami’ar Olabisi Onabanjo da ke garin Sagamu, jihar Ogun za ta fara yajin aiki.

Likitocin na reshen asibitin jami’ar OOUTH sun ce za su shiga yajin aiki a ranar Litinin, 4 ga watan Mayu, 2020, ne saboda gwamnatin Ogun ta ki cika mata wasu bukatunta.

Shugaban kungiyar ARD – OOUTH da kuma sakatarensa sun aikawa mai girma gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun takarda su na sanar da shi wannan mataki da su ka dauka.

Dr. Mutiu Popoola da Dr Tope Osundara sun gabatarwa gwamna Dapo Abiodun wannan takarda ne a ranar Lahadi a garin Abeokuta kamar yadda mu ka samu labari daga NAN.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta NAN ta ce kungiyar ta zargi gwamnatin Ogun da kin daukar matakin da ya kamata duk da irin tarin wasikun da ta rika aika mata a baya.

KU KARANTA: Gwamnatin Zamfara za ta taimakawa Ma’aikata da aron kudin abinci

Likitocin sun ce har yanzu gwamnatin Ogun ta ki fara biyansu sabon tsarin albashin da aka fitar. Haka zalika kungiyar ta ce akwai wasu alawus dinsu da har gobe ba a fara biya ba.

A wasikar da Mutiu Popoola da Tope Osundara su ka rattabawa hannu, sun zargi gwamnatin Dapo Abiodun da zaftare masu wasu kudi daga albashinsu ba tare da wani dalili ba.

Kungiyar ta ARD ta kuma koka da cewa duk hadarin da ‘ya ‘yanta likitoci su ke shiga a asibitocin gwamnatin jihar Ogun, ba a biyansu wasu alawus, sannan babu tsarin inshora a kasa.

ARD ta yi watsi da ikirarin da gwamnatin jihar ta ke yi na cewa ta kara alawus din shiga hadari daga N5, 000 zuwa N15, 000. Kungiyar ta ce yaudara ce kurum ake yi wa jama’an jihar.

Karin 200% da aka yi wa alawus din zai yi aiki ne kurum a watan Afrilu. Bayan haka kungiyar likitocin ta koka da irin tsarin harajin da ta ke kai dabam da na wasu takwarorinta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel