Dakarun Sojoji Sun Ritsa 'Yan Boko Haram a Daji, an Hallaka Miyagu
- Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas sun samu nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno
- Sojojin na rundunar Operation Hadin Kai sun yi nasarar hallaka 'yan ta'adda bayan sun yi musayar wuta yayin wani aikin sintiri
- Wannan na zuwa ne yayin da jami'an tsaro ke kara kaimi wajen kawo karshen ayyukan ta'addanci a jihar Borno
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Dakarun sojoji na sashe na biyu na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai na CJTF sun hallaka ‘yan ta’adda uku na Boko Haram/ISWAP a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun hallaka 'yan ta'addan ne a yayin wani dogon sintiri na fatattakar miyagu a jihar Borno.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Gwara Haka: Jagororin 'yan bindiga sun gwavza fada a Zamfara, an samu asarar rayuka
Sojoji sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram
Majiyoyi sun bayyana cewa aikin sintirin wanda ya kutsa cikin dajin Bulabulin har zuwa yankin Magumeri, ya janyo musayar wuta mai tsanani a kusa da yankin Borno Yesu.
Majiyar ta bayyana cewa bangaren sojojin sama na rundunar Operation Hadin Kai ya bayar da goyon baya ta sama da kuma tsare-tsare na sa ido yayin fafatawar, wanda hakan ya ba dakarun damar mamaye matsugunin ‘yan ta’addan.
"Bayan arangamar, an kashe ‘yan ta’adda uku. Dakarun sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda uku, makamai guda huɗu da aka cika da harsasai, harsasai 120 masu kaurin 7.62mm, gurneti, jakunkunan yaki da sababbin babura guda biyu."
"Tawagar kwararrun sojoji na musamman na ci gaba da mamaye yankin, suna ƙara matsin lamba domin kara fatattakar ‘yan ta’adda, da yanke hanyoyin samun kayayyaki, da hana su ‘yancin yin yawo."
- Wata majiya
Sojoji na kokarin kawar da 'yan ta'adda
Majiyar ta ƙara da cewa, kwarin gwiwar dakarun da kuma kwarewarsu a fagen fama suna nan daram yayin da aikin kawar da ’yan ta’addan ke ci gaba.
Sojojin Najeriya sun ƙara zafafa hare-hare a yankin Arewa maso Gabas domin dawo da zaman lafiya da kuma bada damar komawar al’ummomin da rikicin ya raba da muhallansu cikin aminci.

Source: Original
Karanta karin wasu labaran kan sojoji
- Sojojin Najeriya sun fafata da ƴan bindiga, an cafke wani baƙon ɗan ta'adda a Yobe
- Dakarun sojoji sun yi rugu rugu da 'yan ta'adda, an tura miyagu da dama barzahu
- Karshen alewa: Sojoji sun kashe babban kwamandan Boko Haram da mayaka masu yawa
'Yan bindiga sun hallaka sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun hallaka jami'an sojoji da 'yan sa-kai a jihar Plateau.
'Yan bindigan sun hallaka jami'an tsaron ne bayan sun yi musu kwanton bauna lokacin da suke kan hanyar kai agajin gaggawa.
Mummunan kwanton baunan ya yi sanadiyyar rasa ran sojoji biyu da 'yan sa-kai biyu bayan an kwashi lokaci ana arangama.
Asali: Legit.ng
