Ruwan Sama da Iska Mai Karfi Zai Jawo Ambaliya a Taraba da Jihohi 7 Ranar Lahadi

Ruwan Sama da Iska Mai Karfi Zai Jawo Ambaliya a Taraba da Jihohi 7 Ranar Lahadi

  • Hukumar NiMet ta hango saukar ruwan sama mai karfi da zai iya haddasa ambaliya a wasu jihohi takwas na Najeriya a ranar Lahadi
  • A cewar rahoton, jihohin da ke fuskantar barazanar ambaliya sun hada da Taraba, Niger, Benue, Kwara, Nasarawa, Edo
  • NiMet ta shawarci manoma, matafiya da masu shirya bukukuwa da su kula da sauyin yanayi domin gujewa hadurra da ambaliya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamar yadda ta saba kullum, hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta hasasho ambaliyar ruwa a jihohi takwas na Najeriya.

Hukumar NiMet ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake sa ran za a sheka a ranar Lahadi, 3 ga Agusta, 2025 zai haddasa ambaliya a jihohin.

Ana fargabar ambaliya za ta afku a Taraba, Neja da wasu jihohi 6 a ranar Lahadi
Ambaliyar ruwa ta shiga cikin gari, mutane sun koma tafiya da kafafuwa. Hoto: Adekunle Ajayi/Nur
Source: Getty Images

Hasashen ruwa da ambaliyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar NiMet ta fitar a shafinta na X a daren ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Bikin gargajiya: Gwamnoni 4 za su ba ma'aikata hutu na musamman a Agustan 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen yanayi a jihohin Arewa

NiMet ta fara bude rahotonta da hasashen yanayi na jihohin Arewa, inda ta ce za a samu saukar ruwan sama a wasu yankuna na jihohin Adamawa, Taraba, Borno, Yobe, Bauchi, da Gombe a safiyar Lahadi.

A Arewa ta tsakiya, NiMet ta ce akwai yiwuwar ruwan sama mai karfi ya sauka a Abuja da jihohin Niger, Kwara, Kogi, Nasarawa, da Benue, a safiyar ranar.

Da yammaci zuwa dare kuwa, akwai yiwuwar a samu ruwa hade da iska da tsawa mai karfi a sassa jihohin Adamawa, Borno, Yobe, Kebbi, Kano, Katsina, Zamfara, Jigawa, Taraba, Kaduna, da Bauchi.

A yammacin Asabar din, za a samu ruwan sama mai matsakaicin karfi a Abuja da kuma jihohin Nasarawa, Kwara, Kogi, Plateau, Niger, da Benue.

Hasashen yanayi na shiyyar Kudu

Bayan fitar da hasashen Arewa, hukumar NiMet ta kuma saki bayanai game da hasashen yanayi na jihohin Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kano, Kaduna da sauran jihohin Najeriya da ruwa ya yi ajalin mutane 165 a 2025

A Kudu, NiMet ta ce za a samu ruwa marar karfi a jihohin Ebonyi, Enugu, Ondo, Ogun, Oyo, Akwa Ibom, Cross River, Rivers, da Bayelsa.

Da yammacin Asabar kuma, za a samu ruwan sama a jihohin Ondo, Osun, Ekiti, Oyo, Edo, Abia, Enugu, Anambra, Imo, Ebonyi, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River,a dAkwa Ibom.

Hukumar NiMet ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya zai jawo ambaliya a jihohi 8
Ana zabga ruwan sama da iska mai karfi a wasu sassan Nigeria. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Fargabar ambaliya a jihohin Najeriya 8

Bayan hasashen ruwan sama, hukumar NiMet ta ce ta hango wasu jihohi takwas na iya fuskantar ambaliyar ruwa a ranar Lahadi.

Sanarwar NiMet ta ce:

"Akwai yiwuwar ambaliya ta afku a wasu sassa na jihohin Taraba, Niger, Benue, Kwara, Nasarawa, Edo, Bayelsa, da Cross River States.
"An shawarci daukacin 'yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan yayin da ake ruwa da iska mai karfi, domin ana iya samun hadurra saboda tsawa, kura da sauransu."

NiMet ta kuma shawarci manoma, masu tafiye-tafiye da kuma masu shirya bukukuwa da su ci gaba da bibiyar rahotannin hasashen yanayi daga hukumar.

Ambaliya ta rusa gine-gine a Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri, inda mazauna wuraren da abin ya shafa suka fara hijira.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya fara gwangwaje jihohin Arewa da titunan jiragen kasa

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da afkuwar ambaliya a Bulumkutu da Gomari, har ta kai an tura jami’ai don ceto mutane kuma a hana sata.

Wannan ambaliya ta biyo bayan ruwan sama na tsawon sa’o’i uku, wanda ya jawo rushewar gine-gine takwas, a cewar 'yan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com