Saniya Ta Sangarce a Gidan Gwamnati, Manyan Jami'ai Sun Tsere, Ta Raunata Mutane

Saniya Ta Sangarce a Gidan Gwamnati, Manyan Jami'ai Sun Tsere, Ta Raunata Mutane

  • Wata saniyar da aka kawo don yanka ta addabi ma’aikacin Gidan Gwamnati a Asaba, inda ta jikkata mutane da dama
  • Wani ma’aikaci dan shekara 30 da ya kokarta kama saniyar ya samu munanan raunuka, an garzaya da shi asibiti cikin gaggawa.
  • Har ila yau, wani mai girki mai suna Peter shi ma ya jikkata, sai dai gwamnatin Delta bata fitar da sanarwa kan lamarin ba har yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Asaba, Delta - An samu tashin hankali a gidan gwamnati bayan saniya ta yi barna tare da jawo raunuka ga wasu ma'aikata

Lamarin ya faru a karshen mako a Gidan Gwamnati na Asaba a jihar Delta lokacin da saniya ta kai hari ta jikkata wani ma’aikaci.

Saniya ta illata wasu mutane a gidan gwamnati
Saniya ta balle a gidan gwamnatin Delta inda ta raunata mutane. Hoto: Delta State Government House.
Source: Facebook

Barnar da saniya ta yi a gidan Gwamnatin Delta

Kara karanta wannan

Cin amana: Magidanci ya kama matarsa tsirara da wani namiji a gado, ya ɗauki mataki

The Guardian ta ce an kawo saniyar ce domin a yanka ta inda ta tsere daga hannu ta afka wa mutane da ba su ji ba ba su gani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce saniyar ta jikkata da dama cikin firgici da ruɗani wanda ma'aikata suka nemi mafaka domin tsira da rayukansu.

Daya daga cikin wadanda suka jikkata, wani namiji dan shekaru 30, ya samu munanan raunuka bayan da saniyar ta bugi jikinsa.

An garzaya da shi dakin gaggawa na asibitin Gidan Gwamnati domin kulawa, bisa bayanin wata majiya daga wajen da abin ya faru.

An kai wasu asibiti a gidan gwamnati bayan harin saniya
Saniya ta jikkata wasu a gidan gwamnatin Delta bayan harin saniya. Hoto: Legit.
Source: Original

Delta: An bayyana wadanda abin ya shafa

Majiyar ta kara da cewa wani ma’aikaci mai suna Peter, wanda shi ne mai girki a Gidan Gwamnati, shi ma ya samu raunuka, cewar rahoton Daily Post.

Wata majiya ta ce:

“Saboda tsananin raunin da ya samu, daga baya aka kai shi wani asibiti daban inda yake fafutukar ceton ransa.
“Masu yankan saniya guda biyu da aka fara kiran su sun kasa kama ta, suka tsere. Wanda ya fi jikkata shi ne aka kira daga baya."

Babu sanarwa har yanzu daga hukumomi a Delta

Kara karanta wannan

Musulmi sun fusata da dodanni suka farmaki limamin Musulunci, an roki gwamna

Har zuwa lokacin da aka rubuta wannan rahoto, Gidan Gwamnatin bai fitar da wata sanarwa ta hukuma ba kan faruwar lamarin wanda ya firgita mutane da dama da ke gidan gwamnati.

Duk da rahotanni sun bayyana cewa ballewa saniyar ta yi, wasu na ganin akwai sakaci a lamarin saboda illar da hakan ke da shi wanda ya nuna akwai rashin kulawa yayin daure saniyar.

Tsohon gwamna ya koka kan matsin tattalin arziki

Mun ba ku labarin cewa tsohon Gwamnan Delta, James Ibori, ya ba Jami’ar Igbinedion gudunmawar Naira miliyan 100 domin tallafa mata da ci gaban ilimi.

Ibori ya ce matsin tattalin arziki ne ya hana shi yin abin da ya fi haka don inganta jami’ar a Okada da ke jihar Edo a Kudancin Najeriya domin ba da gudunmawa game da ci gaban ilimi.

Ya yaba da gagarumin aikin Esama Gabriel Igbinedion wajen kafa makarantu daga matakin firamare har zuwa jami’a a Najeriya inda ya ce zai ci gaba da ba da gudunmawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.