Mutanen Gari da 'Yan Sanda Sun Yi Arangama a Abuja, an Samu Asarar Rai

Mutanen Gari da 'Yan Sanda Sun Yi Arangama a Abuja, an Samu Asarar Rai

  • Mutanen gari sun yi fito na fito da jami'an tsaro na 'yan sanda a babban birnin tarayya Abuja
  • Arangamar ta auku ne bayan da wasu masu kwacen fili suka yi kokarin shiga kauyen Kuchibiyi da ke karamar hukumar Bwari
  • Lamarin ya jawo ran wani mutum daya, yayin da wasu kuma daban suka samu raunuka bayan 'yan sanda sun yi harbi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - An samu asarar ran mutum daya bayan da rikici ya barke tsakanin mazauna kauyen Kuchibiyi da jami'an 'yan sanda a Abuja.

Wasu biyu kuma sun jikkata sakamakon harbin bindiga, biyo bayan rikicin wanda ya auku a karamar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya Abuja.

'Yan sanda sanda sun yi harbi
Mutanen gari sun yi artabu da 'yan sanda a Abuja Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Wani mazaunin ƙauyen Kuchibiyi, Samuel Dangana, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust ta wayar tarho a ranar Asabar, 2 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Gwara Haka: Jagororin 'yan bindiga sun gwavza fada a Zamfara, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen gari sun gwabza da 'yan sanda

Ya ce rikicin ya fara ne lokacin da wasu masu ƙwace fili tare da wasu jami’an ‘yan sanda daga ofishin Byazhin suka kutsa cikin ƙauyen domin su mamaye wani fili.

Samuel Dangana ya ce mazauna ƙauyen bayan da suka hango jami’an tsaron, sai suka taru da gaggawa suka rufe hanya don hana masu ƙwacen filin shiga wajen.

Ya ƙara da cewa rikici ya barke ne lokacin da mazaunan ƙauyen, suka fuskanci jami’an tsaron da sanduna da duwatsu a hannunsu, lamarin da ya sa jami’an tsaron suka fara harba hayaki mai sa hawaye da harsasai kai tsaye a kansu.

"Masu kwacen filin sun shigo tare da wasu ‘yan sanda suna ƙoƙarin yanka wani filin, amma mazaunan ƙauyen suka toshe hanya don hana su shiga."
"Daga nan sai muka fara jin harbin bindiga da hayaki mai sa hawaye. Daya daga cikin mazaunan ƙauyen ya mutu sakamakon harbin bindiga, yayin da wasu biyu kuma suka ji rauni."

Kara karanta wannan

Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya

- Samuel Dangana

Dangana ya ce mutanen biyu da suka ji rauni suna karɓar magani a wani asibiti da ke garin Bwari.

'Yan sanda sun yi fada da mutanen gari a Abuja
Mutum 1 ya rasu sakamakon arangama da 'yan sanda a Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Kansilan yankin Byazhin/Kuchibiyi a karamar hukumar Bwari, Hon. Dogara J. Ahmed, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa mutum guda ya rasu, yayin da biyu kuma suka ji rauni a rikicin, kodayake har yanzu bai samu cikakken bayani ba dangane da abin da ya faru.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Adeh Josephine, ta ce an kama wasu mutane biyo bayan rikicin da ya faru a ƙauyen Kuchibiyi da ke Bwari.

Ta ce an kama wasu da ake zargi, kuma bincike na ci gaba da gudana, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da hakan.

Rikicin kabilanci ya barke a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu barkewar rikicin kabilanci tsakanin Fulani da 'yan kabilar Gwari a Abuja.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP, an tura miyagu barzahu

Rikicin ya barke bayan takaddama ta auku tsakanin wani manomi da bafillatani kan tsallaka gona.

Mummunan lamarin wanda ya auku a karamar hukumar Gwagwalada ya yi sanadiyyar rasuwar mutum daya tare da kona gidaje akalla guda 35.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng