Malaman Jinya Sun Cimma Matsaya kan Janye Yajin Aiki a Fadin Najeriya
- Kungiyar malaman jinya da unguwar zoma ta kasa ta fitar da sanarwa kan yajin aikin gargadi da ta shiga
- A ranar Asabar, 2 ga watan Agustan 2025, kungiyar ta dakatar da yajin aikin wanda ta kwashe kwanaki hudu tana yi
- Ta bayyana cewa ta janye yajin aikin ne bayan sun samu fahimtar juna tsakaninta da gwamnatin tarayya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar malaman jinya da ungonzoma ta kasa (NANNM) ta dakatar da yajin aikin gargadi da ta fara a fadin ƙasar nan.
Kungiyar NANNM ta janye yajin aikin ne bayan ta kwashe kwanaki hudu tana yi.

Source: UGC
Mataimakin sakataren kungiyar na kasa, Chidi Aligwe, ne ya bayyana hakan ga jaridar The Punch a ranar Asabar, 2 ga watan Agusta, 2025.
Ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin ne a ranar Asabar, bayan wata ganawa ta intanet da shugabannin NANNM na kasa suka gudanar.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Jam'iyyar ADC ta dakatar da ɗan majalisar tarayya mai ci a Kogi
Malaman jinya sun tsunduma yajin aiki
A ranar Laraba da ta gabata ne malaman jinya da unguwar zoma a Najeriya suka fara yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai don matsa lamba kan cika wasu buƙatu da suka dade suna nema.
A ranar Juma’a, ƙungiyar ta gana da ma’aikatar lafiya da jin daɗin jama’a ta tarayya, ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati, ma’aikatar kwadago, ofishin Akanta janar na tarayya, hukumar albashi da fansho ta kasa, da sauran masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan cika buƙatun mambobinta.
An dakatar da yajin aikin kungiyar NANNM
"An dakatar da yajin aikin. Malaman jinya da unguwar zoma su koma bakin aikinsu nan take."
- Chidi Aligwe
Jaridar Leadership ta ce wata takarda mai taken “Dakatar da ci gaba da yajin aiki na malaman jinya a fadin kasa” wadda shugaban kungiyar na kasa, Haruna Mamman, da sakatare, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu, ta tabbatar da wannan ci gaba.

Kara karanta wannan
'Ba mu janye ba,' malaman jinya sun 'kunyata' ministan lafiya kan batun yajin aiki
A cikin takardar, an bayyana cewa majalisar zartarwa ta kasa (NEC) ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne bayan ta yi nazari mai zurfi kan yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma da kuma tsarin aiwatarwa tare da takamaiman lokacin cika su.

Source: Getty Images
Wani bangare na takardar na cewa:
"NEC ta yaba da matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka wajen amsa buƙatu tara da ƙungiyar NANNM ta gabatar, musamman yadda aka ƙayyade lokutan aiwatar na kowanne daga cikin buƙatun.”
"Dangane da yarjejeniyar da aka cimma a hukumance, tare da bin ka’idar tattaunawa da girmama juna, NEC ta dakatar da yajin aikin da ake yi a fadin ƙasa nan take."
NEC ta umurci shugabancin ƙasa na ƙungiyar da su ci gaba da sa ido kan yadda ake aiwatar da yarjejeniyar da aka sanya wa hannu tare da bin diddigin yadda gwamnati ke bin tanadin lokaci da aka tsara.
Malaman jinya sun musanta janye yajin aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa malaman jinya da unguwar zoma ta musanta batun cewa ta yanye yajin aikin gargadin da ta shiga.
Kungiyar ta bayyana cewa ko kadan ba ta janye yajin aikinda ta shiga domin neman gwamnati ta biya mata bukatunta ba.
Ta bayyana cewa makasudin tsunduma yajin aikin shi ne neman gwamnati ta cika mata abubuwan da ta dade tana nema.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng